Manyan Jiga-Jigan PDP a Jihar Kwara Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Manyan Jiga-Jigan PDP a Jihar Kwara Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Ƙasa da wata daya kafin buga gangar zabe a Najeriya, jam'iyyar PDP mai adawa ta gamu da tasgaro mai girma a jihar Kwara
  • Manyan jiga-jigai ciki har da hadiman Bukola Saraki da Abdulfatah Ahmed sun sauya sheka zuwa APC a karshen mako
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris, 2023, INEC ta tsara gudanar da zabukan wannan shekarar

Kwara - Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP daga sassan kananan hukumomi huɗu da suka haɗa mazabar Sanatan Kwara ta tsakiya sun sauya sheƙa zuwa APC a ƙarshen makon nan.

Guguwar ta fi dibar mutane a gundumar Ibagun, ƙaramar hukumar Ilorin ta gabas, inda tsoffin hadiman Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa da makusantan tsohon gwamna, Abdulfatah Ahmed, suka koma APC.

Sauya sheka a Kwara.
Manyan Jiga-Jigan PDP a Jihar Kwara Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Hoto: leadership
Asali: UGC

Jaridar Leadership tace daga cikin manyan 'yan siyasan da suka fice PDP tare da dumbin magoya bayansu har da, Barista Shehu Salaudeen Ismail, tsohon hadimin Abdulfatah da Alhaji Oladimeji Ayinla, tsohon hadimin Saraki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan PDP

Bayanai sun nuna cewa jiga-jigan sun tabbatar da shiga APC a hukumance a wurin Ralin kamfe da ya tara dubbannin magoya bayan APC wanda ya gudana a Ibagun, Okele, Ilorin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Legit.ng ta gano cewa daga cikin kuoshin PDP da suka ja ragamar ɗaruruwan magoya bayansu zuwa APC a taron sun haɗa da, Babatunde Aremu, Ayuba AbdulGaniyu, da AbdulGafar Adekunle.

Sauran sun ƙunshi, Yunus Kayode Ibrahim, Hammed Ayinla, Adam Ayinla, Dauda isiaka Amuyankan, Sikiru Soliu Amuyankan, Kamaldeen Bushari, Toheeb Abdullah, Musa Ajibola da sauransu.

Ba za'a nuna muku wariya ba - Salahu

Mashawarci na musamman ga gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, na bamgaren dabaru, Alhaji Saadu Salahu, ne ya tarbi jiga-jigan masu sauya shekar.

Hadimin gwamnan ya tabbatar masu da cewa ba za'a nuna musu wariya tsakaninsu da tsoffin mambobin APC, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Ta Ƙarewa Kwankwaso, Wasu Manyan Jiga-Jigan NNPP Sun Sauya Sheka Zuwa PDP

Salahu ya kuma gode wa masu sauya shekar bisa hango ayyukan Alherin gwamna AbdulRazaq a kowane bangare da suka haɗa da tallafawa matasa da mata, wanda ya ja hankalinsu zuwa APC.

Ba Zan Bar Gidana Na Koma Dauji ba - Sanata Gobir

A wani labarin kuma Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa ya yi karin haske kan jita-jitar ya gama shirin komawa PDP

Sanata Ibrahim Gobir mai wakiltar Sakkwato ta gabas ya bayyana cewa yana nan daram a jam'iyyar APC sabanin jita-jitar da ake yaɗawa a kansa.

Sanatan ya nemi tikitin takarar gwamnan APC a zaben fidda gwani da ya gudana a Sakkawato amma bai samu nasara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel