Dalilin da yasa nake goyon bayan Tinubu duk da ina PDP, Sanata Nnamani

Dalilin da yasa nake goyon bayan Tinubu duk da ina PDP, Sanata Nnamani

  • Sanatan Enugu kuma mamban jam'iyyar PDP, Chimaroke Nnamani, ya yi bayani kan dalilinsa na goyon bayan Tinubu
  • Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu ya ce PDP ba ta da adalci da daidaito tun da ta mika tikitin shugaban kasa ga ɗan arewa
  • Sanatan ya ce kwansutushin din PDP ya tanadi tsarin raba manyan mukamai tsakanin arewa da kudu

Abuja - Sanatan jam'iyyar PDP daga jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, yace ya yanke shawarin komawa wurin Bola Tinubu, mai neman zama shugaban ƙasa a APC ne saboda PDP ta yi rashin adalci.

Jaridar Premium Times ta rahoto Sanatan na cewa ya yi haka ne saboda PDP ta karya kundin mulkinta bayan ta take tanadin tsarin mulkin karɓa-karba.

Nnamani, tsohon gwamnan jihar Enugu ya yi wannan bayanin ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Sakataren NNPP Ya Fallasa Asirin Kwankwaso, Ya Faɗi Abubuwa Da Yawa

Chimaroke Nnamani.
Dalilin da yasa nake goyon bayan Tinubu duk da ina PDP, Sanata Nnamani Hoto: Chimaroke Nnamani
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa a kwanan nan ne jam'iyyar PDP ta ƙasa ta dakatar da Sanata Nnamani kan abinda ta kira zagon ƙasa da cin amanar jam'iyya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma Sanata Nnamani yace kwansutushin ɗin PDP ya tanadi raba manyan kujerun siyasa tsakanin arewa da kudu domin tabbatar da adalci da kuma daidaito.

Punch ta rahoto Sanatan na cewa:

"Duk da kowa ya san akwai bukatar karba-karba na manyan mukaman siyasa tsakanin al'ummar ƙasar nan, Kwansutushin ɗin PDP ya nuna ƙarara a bi tsarin karba-karba a mukaman jam'iya da gwamnati domin tafiya da kowa."
"Haka na duk da shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya tabbatar da kudirinsa na murabus idan ɗan arewa ya zama ɗan takarar shugabna ƙasa, jam'iyyar ta jingine tanadin doka kuma ta juya batun sama ya koma ƙasa."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Yan Daba Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamnan PDP

"Idan baku manta ba a 2019, PDP ta bar arewa ta nemi takara a zaben fidda gwani a Patakwal, jihar Ribas wanda kuma Atiku ya samu nasara. An yi tsammanin a 2023 PDP zata barwa kudu tikitin shugaban kasa."

"Amma jam'iyyar ta yanke shawarin barin kofa a bude ga yan kudu da arewa su nemi takara. A wani yanayin karfafa da murɗiya aka ayyana Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe tikitin shugaban kasa," inji Nnamani.

Zaben Atiku ya fusata mambobin PDP

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sakamakon zaben fidda gwanin ya fusata da yawan mambobin jam'iyyar ciki har da gwamnonin G-5 waɗanda suka tsaya kai da fata sai an yi biyayya ga tsarin karba-karba.

A cewar Nnamani, abinda PDP ta yi ya nuna rashin adalci da daidaito ƙarara domin ko a hankalce bai dace mulki ya cigaba da zama a arewa ba bayan Buhari ya gama zango biyu a 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Babbar Kotu Ta Tsige Sanata Mai Ci Daga Kujerarsa Kan Laifi 1

Meyasa yake goyon bayan Tinubu?

Sanatan ya yi ikirarin cewa domin tabbatar da daidaito tsakanin kudu da Arewa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bude kofar da Tinubu ya zama ɗan takarar APC.

"Bayan nazari cikin natsuwa game da batun, na ɗauki Bola Tinubu matsayin ɗan takarar da na fi so daga kudu da zai iya cika burinmu a 2023," inji shi.

A wani labarin kuma Manyan Jiga-Jigan PDP Da Dubannin Mambobi Sun Koma APC a jihar Kwara

Guguwar ta fi dibar mutane a gundumar Ibagun, ƙaramar hukumar Ilorin ta gabas, inda tsoffin hadiman Bukola Saraki, da tsohon gwamnan Kwara suka ja tawaga zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262