Bola Tinubu: Yadda Nayi Ta Lallabar Buhari, Har Aka Kara Wa’adin Canza Tsohon Kudi
- Asiwaju Bola Tinubu ya bada gudumuwa wajen karin kwanakin da bankin CBN ya yi na canza kudi
- ‘Dan takaran na jam’iyyar APC ya ce ya yi ta neman wannan alfarmar a wajen Muhammadu Buhari
- Bola Tinubu ya ce a karshe shugaban kasa ya saurare su, ya yarda CBN su kara wa’adin ‘yan kwanaki
Edo - Asiwaju Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC ya sake magana a kan canjin kudin da babban bankin Najeriya na CBN ya yi.
A ranar Lahadi, 29 ga watan Junairu 2023, Vanguard ta rahoto Asiwaju Bola Tinubu yana mai cewa canjin manyan takardun Nairori zai fi shafan ‘matanmu’.
‘Dan takaran na jam’iyyar APC mai mulki ya ce matansu da ke saida yalon bello, karas da gasasshiyar masara ne za su shan wahalar tsarin nan na CBN.
Bayanin nan ya fito daga bakin Bola Tinubu yayin da ya ziyarci birnin Benin a jihar Edo domin tallata takararsa da kuma ganawa da wasu masu ruwa da tsaki.
Jaridar ta ce ‘dan takaran ya gabatar da manufofinsa ga jagororin siyasa, matasa da ‘yan kwadago.
Tinubu a fadar Oba na Benin
Da ya je fadar Oba na Benin, Oba Ewuare II tare da sauran Sarakunan jihar, Tinubu ya jinjinawa Muhammadu Buhari a kan tsawaita wa’adin karbar tsohon kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabin da ya yi a gaban Mai martaba Oba Ewuare II, ‘dan takaran ya ce kokarin rokon a kara tsawon wa’adin ya jawo ya iso taron da yamma a makare.
Fadi-tashin Tinubu a gaban Buhari
“Ba da gan-gan na makara wajen isowa ba, saboda siyasar kasa ne.
Wasu ‘yanuwanmu da matanmu da ke saida yalo, karas da gasasshiyar masara su na bukatar kudi, su na bukatar Naira.
A dalilin haka, idan aka soke amfani da Naira a yadda ake, kuma ba tsoma bai ba, mun gaza sauke nauyin da yake kanmu.
Mun yi kwanaki uku zuwa hudu a kan wannan, sai kwatsam yau shugaban kasa ya yi na’am, ya ce zai duba bukatarmu."
- Bola Tinubu
Blue Print ta rahoto tsohon Gwamnan na Legas yana bayanin yadda Buhari ya girmama shi, ya amsa rokon da ya kai masa, ya ce ya yi farin ciki da hakan.
Tinubu yake cewa ya yi ta zuwa ya je ya dawo a kan maganar, a karshe duk da bai samu yadda yake so ba, gwamnatin Buhari ta amince ta kara ‘yan kwanaki.
Wani jami'in banki a Zariya, Umar Mahmud Hamzah ya shaida mana cewa duk da karin wa'adin, ana fuskantar kalubale a dalilin sauyin kudi da CBN ya yi.
Ma'aikacin ya ce duk wani tsohon kudi da ya shiga banki ba zai fito ba, amma ya bayyana cewa ana daukar mataki domin samun kananan takardun kudi.
Kayode Fayemi v Kayode Otitoju
Duk da ana tare a jam’iyyar APC, an ji labari tsohon Gwamna Kayode Fayemi ya dauki hayar Lauya, ya yi karar wani jigo a jam’iyya mai mulki, Kayode Otitoju.
Tsohon Gwamnan na jihar Ekiti yana so Alkali ya tursasa Kayode Otitoju, ya biya shi N250m bisa zargin ‘dan siyasar ya ci masa zarafi a wata hira a gidan talabijin.
Asali: Legit.ng