Ku Kula da Hatsarin Da Ke Gaba: Primate Ayodele Ya Gargadi Tinubu, Atiku da Obi

Ku Kula da Hatsarin Da Ke Gaba: Primate Ayodele Ya Gargadi Tinubu, Atiku da Obi

  • Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Ayodele, ya aika gagarumin gargadi ga Bola Tinubu, Peter Obi da Atiku Abubakar gabannin zabe mai zuwa
  • Ayodele ya ce akwai kalubale a gaban yan takarar yayin da ranar zaben ke kara gabatowa, yana mai cewa ya kamata arewa ta zama wurin da za su mayar da hankalinsu
  • Ya ce yan arewa za su yi Atiku amma zai fuskanci badakaloli, kawunan 'cabals' zai rabu kan Tinubu

Primate Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritualya aika gagarumin gargadi ga manyan yan takarar shugaban kasa gabannin babban zaben 2023.

A cewar malamin addinin, Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na Labour Party (LP) za su fuskanci matsaloli a gaba, jaridar PM News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya San Cewa Atiku Ne Zai Zama Shugaban Kasa, In Ji Shu'aibu

Atiku, Tinubu da Obi
Ku Kula da Hatsarin Da Ke Gaba: Primate Ayodele Ya Gargadi Tinubu, Atiku da Obi Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Hasashen da aka yi kan Atiku, Tinubu da Obi gabannin 2023

Ayodele ya bayyana hasashen nasa ne a cikin wata sanarwa daga hadimin labaransa, Osho Oluwatosin, inda ya yi magana game da matsalolin da yan takarar shugaban kasar za su fuskanta a zaben 2023 yayin da ya basu mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar faston, Peter Obi na bukatar yin aiki sosai a arewa sannan ya wayar da kan magoya bayansa kan muhimmancin karbar katunan zabensu, yana mai cewa ba lallai bane yawancin matasa su zabe shi.

Ya bukaci tsohon gwamnan na jihar Anambra da kada ya yarda goyon bayan tsoffin yan siyasa ya dauke masa hankali da kuma kin gayawa magoya bayansu su je su karbi katunan zabensu.

Hasashen Primate Ayodele

Game da Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar zai samu goyon bayan dattawan arewa amma akwai badakaloli da dama a gaban shi, rahoton Within Nigeria.

Kara karanta wannan

Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Bayyana Abinda Zasuyi A Kwana 100 Farko

Kan takarar Tinubu, Primate Ayodele ya ce kawunan na kewaye da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wato 'cabals' za su rabu a kan lamarinsa.

Ya ce takararsa zai fuskanci turjuya daga arewa, kudu maso gabas da kudu maso kudu amma ya bukace shi da ya yi aiki tukuru.

Ina so na zama matar shugaban kasa Bayarabiya ta farko, Titi Atiku

A wani labarin, matar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Titi Atiku Abubakar, ta bayyana cewa tana son ta zama Bayarabiya ta farko da za ta hau kujarar matar shugaban kasa.

Bisa wannan dalilin ne ta roki al'ummar yankin arewa maso yamma da su zabi mijinta domin ta cika wannan buri nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng