Ina So Na Zama Matar Shugaban Kasa Bayarbiya Ta Farko: Titi Atiku Ta Roki Masu Zabe

Ina So Na Zama Matar Shugaban Kasa Bayarbiya Ta Farko: Titi Atiku Ta Roki Masu Zabe

  • Titi Atiku Abubakar ta ce tana so ta rusa wannan tarihin na rashin samar da matar shugaban kasa Bayarbiya tun bayan dawowar damokradiyya
  • Uwargidar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ta ce har yanzu mutanen kudu maso yamma basu samar da matar shugaban kasa ba kuma ita za ta rusa wannan tarihin
  • A cewar Titi, ya kamata dukkanin Yarbawan Najeriya su marawa takarar mijinta baya domin bata damar cimma burinta

Matar Atiku Abubakar, Titi ta yi kira ga al'ummar Yarbawa da su tabbata sun zabi mijinta wanda ke neman takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa a wata hira da aka yi da ita a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, Titi ta bayyana cewa har yanzu Yarbawa basu samar da uwargidar shugaban kasa ba tun bayan dawowa damokradiyya a 1999.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Kan Yunkurin Da PDP Ta Yi Na Haramtawa Tinubu Takara

Titi Atiku
Ina So Na Zama Matar Shugaban Kasa Bayarbiya Ta Farko: Titi Atiku Ta Roki Masu Zabe Hoto: PDP
Asali: UGC

Da take rokon mutanen yankin kudu maso yamma kan su goyawa mijinta baya, Titi ta ce tana so ta zama matar shugaban kasa Bayarbiya ta farko.

A hirar tasu wacce BBC Yoruba ya gudanar, Titi ta ba mutane tabbacin cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aikin bayar da agaji a lamuran da suka shafi mata da yaki da fataucin kananan yara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamanta:

"Tun bayan dawowar mulkin farar hula a 1999, babu Bayarbiyar da ta zama matar shugaban kasa a kasar nan. Ina so na zama Bayarbiya ta farko.
"Ina so Yarbawa su marawa takarar Atiku baya. Nasarar Atiku zai sa na zama matar shugaban kasar nan."

Har ila yau da take bayyana cewa mijinta zai hada kan mutanen Najeriya idan aka zabe shi, Titi ta ce Atiku na son yiwa al'umma hidima.

Kara karanta wannan

2023: Ku zabi mijina, Idan ya gaza laifi na ne, matar Atiku ta roki a hukunta ta

Ta kara da cewar:

"A lokacin samartakarsa, ya yi karatu a kyauta. Gwamnati ta dauki nauyin karatunsa sannan ta bashi tallafi. Gwamnati ta kuma bashi aiki.
"Bayan ya wuce wannan matakin, sai ya fahimci cewa gwamnati ta yi masa abubuwa masu kyau. Don haka, ya kudirci aniyar saka alkhairin ga yan Najeriya duba ga abun da kasar ta yi masa.
"Mijina ya ce zai yi abubuwa biyar ga Najeriya. Ya ce zai gyara Najeriya. Babu hadin kai a kasar nan. Kasar na cikin wani hali a yanzu."

Tushen Titi

Da take tunatar da mutanen cewa ita diyarsu ce, matar Atiku ta ce Najeriya ta fi hadin kai baya fiye da yanzu.

Ta ce:

"Ni yar jihar Osun ce. A baya, Kiristoci da Musulmai na yin abubuwa a tare. Iyayena sun bar ni na aure shi. Amma yanzu, ba mu san ina duniyar ta dosa ba. Mijina ya ga dukkanin abubuwan kuma ya ce ya na so ya dawo da Najeriya tafarkin hadin kai."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sabuwar Kungiyar ‘Yan Ta’adda Ta Bullo a Kudu, Sun Gindaya Sharadi Kafin Su Bari ayi Zabe

Arewa ba za ta yi la'akari da addini wajen zaben magajin Buhari ba, APC

A wani labarin kuma, jam'iyyar APC ta bayyana cewa al'ummar yankin arewacin Najeriya ba za su duba addini ba wajen zaben shugaban kasa a zaben 2023.

Hakan martani ne ga ikirarin da PDP ta yi na cewa yan arewa ba za su yi Bola Tinubu ba saboda Musulmin bogi ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel