Manya Shugabannin Yan Takarar Shugaban Kasar Nigeria Sun Bayyana Abinda Zasuyi A Kwana Darin Farko

Manya Shugabannin Yan Takarar Shugaban Kasar Nigeria Sun Bayyana Abinda Zasuyi A Kwana Darin Farko

  • Yan takarar shugaban kasa sunyi bajakolin abubuwan da zasuyi a kwana darin farko na gwamnatinsu
  • Wasu sun bayyana harkar tsaro, wasu hadin kan kasa da kuma amfani da dabaru dan inganta harkokin mulki
  • Shi kuwa Tinubu yace zai tabbatar da yan makarantar firamare zasu ci su koshi

Abuja - Manyan yan takarar shugaban kasa wanda zasu faffata a watan Fabairun wannan shekarar sun bayyana abunda zasuyi a kwana darin farko na gwamnatinsu idan sukayi nasara.

Manyan yantakarar da suka hada da Peter obi na jam'iyyar LP, da Atiku Abubakar na PDP, da Rabi'u Musa Kwankwaso na NNPP sai kuma dan takarar APC Bola Ahmed Tinubu

Yan takarar shugaban kasar sun bayyana hakan ne a lokacin da suke tattaunawa da jaridar Daily Trust.

Obi Yayi alkawarin tabbatar da hadin kan Nigeria

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Fitaccen Malamin Addini Na Najeriya Ya Bayyana Yan Takarar Shugaban Kasa Da Za Su Fadi Zabe

A yayin da yake bayani kan mulkinsa, Obi yace zai tabbatar da hadin kan Nigeria in aka zabeshi.

Obi wanda yai bayani a cikin wani faiain bidiyon yace zai tabbatar da tsaro bayan hadin kan yan Nigeria.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben
Manya Shugabannin Yan Takarar Shugaban Kasar Nigeria SUn Bayyana Abinda Zasuyi A Kwana Darin Farko Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ya kara da cewa lalle za'a samu tsaro, sannan manoma zasuyi noma ba tare da fargaba ba sannan zasu samarwa da kasa abinda take bukata.

Atiku ya ce zai tabbatar da gwamnati mai tsafta da hadin kan kasa

Dan takarar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yace inda gwamnatinsa zata dosa shine maida hankali wajen tabbatar da ka'idojin gwamnati da hadin kai da kuma samar da doka da oda. Rahotan Leadership

Atiku yace:

"A gani na, wannan zaben da za'ayi, nine wanda nafi cancantarsa, da kuma dacewa da akasar nan dan ingancinta"

Zamu ciyar da 'ya'yanku, Tinubu ya tabbatarwa da yan NIgeria

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Peter Obi Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC, yace a kwana darin farko zasu tabbatarwa da yan Nigeria sun ciyar da 'ya yansu

Tinubu yace:

"Muna bukatar yan Nigeria su sanya ya yan su sun tura su makaranta, sabida zasu ci su koshi, har ma su tafi da shi gida"

Shi kuwa Kwankwaso cewa yace tsaro zai tabbatar

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Kwankwaso yace zai tabbatar da a kwana darin farko, na yakar tsaro da harkar fasahar zamani.

Kwankwaso yace:

"Kamar yadda na tsaya a gabanku yanzu, muna da mataltsalu masu yawa wanda suka shafi tsaro, a kowanne bangaren kasar nan, dan haka zamu inganta harkokin soji.

A yayin da taron da hukumar kasar Amurka ta shirya da hadin gwiwar Cathalotic Archbishop na Abuja, John Cardinal Oneiyenkan, wanda aka shirya dan tattaunawa da yan takarar shugaban kasa.

Ambasadar Amurka a Nigeria, Mary Beth Leonard tace kasar amurak ta hana da tsari mai kyau da kuma tabbacin yin sahihin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel