2023: APC Ce Zata Lashe Zabe Duk Da Zagon Kasar Da Ake Mana, Tinubu

2023: APC Ce Zata Lashe Zabe Duk Da Zagon Kasar Da Ake Mana, Tinubu

  • Yan makonni kafin zaben shugaban kasa na 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya ci zabe ya gama
  • Dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar APC ya ce da izinin Allah shine zai zama zakarar gwajin dafin zabe mai zuwa duk da zagon kasar da ake masa
  • Tinubu ya ba al'ummar Zamfara tabbacin cewa gwamnatinsa za ta bunkasa harkar noma da hakar ma'adinai a jihar

Zamfara - Gabannin babban zaben 2023 mai zuwa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya jaddada cewar jam'iyyarsa ce zata lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu duk da zagon kasar da ake mata.

Tinubu wanda ya ziyarci Zamfara a ranar Asabar, 28 ga watan Janairu, ya bayar da tabbacin inganta jihar ta bangaren noma da hakar ma'adinai idan ya zama shugaban kasa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

Bola Tinubu
2023: APC Ce Zata Lashe Zabe Duk Da Zagon Kasar Da Ake Mata, Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Da yake jawabi ga taron jama'a a gangamin kamfen dinsa a Gusau, jihar Zamfara, Tinubu ya ba da tabbacin cewa duk da zagon kasar da ake yi wa jam'iyyarsa ita ce za ta lashe zabe da izinin Allah.

New Telegraph ta nakalto Tinubu yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Koda dai an shirya matakan kawo tsaiko ga gangamin kamfen dina, amma daga yadda nake kara yin suna a fadin kasar, zan lashe zabe."

Ya ci gaba da cewa:

"Bari na ba ku tabbacin cewa za a ba bangaren noma kulawa da kyau a gwamnatina. Duk da zagon kasar da ake mana, APC zata lashe zabe.
"Za a sarrafa dumbin ma'adinan da ke Zamfara da kyau don amfanin gwamnati da al'umma."

Ya yaba ma magoya bayan APC kan gagarumin liyafar da aka yi wa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Yan Kwanaki Kafin Zabe, Tinubu Ya Daukarwa Iyaye Gagarumin Alkawari Da Zai Cika Masu a Kan 'Ya'yansu

Da farko, shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu ya nuna farin ciki kan dandazon magoya bayan jam'iyyar da suka fito don yi wa tawagar kwamitin kamfen din shugaban kasar maraba da zuwa Zamfara.

Matawalle ya ba tawagar kamfen din tabbacin cewa APC za ta kawo Zamfara da sauran jihohin arewa a zabe mai zuwa da izinin Allah.

A wani labarin, Bola Tinubu ya sha alwashin cewa idan ya lashe zabe a 2023, abinci zai yawaita a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel