Bamu Kori Ministan Shugaba Buhari Daga Inuwar Jam'iyya Ba, APC

Bamu Kori Ministan Shugaba Buhari Daga Inuwar Jam'iyya Ba, APC

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom ta musanta wasikar da ke yawo cewa ta dakatar da Ministan harkokin Neja Delta
  • Shugaban APC na jihar, Stephen Ntukekpo, yace takardan ta bogi ce domin basu taba ko da tunanin dakatar da Ministan ba
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da APC ta kori tsohon hadimin shugaban ƙasa bisa zargin cin amana

Akwa Ibom - Jam'iyyar APC reshen jihar Akwa Ibom ta ankarar da ɗaukacin al'umma game da wata takardar bogi dake yawo a sohiyal midiya.

Premium Times ta tataro cewa takardar ta yi ikirarin cewa APC ta kori Ministan harkokin Neja Delta na yanzu, Umana Ukon Umana daga inuwar jam'iyyar.

Ministan Neja Delta.
Bamu Kori Ministan Shugaba Buhari Daga Inuwar Jam'iyya Ba, APC Hoto: Premiumtimesng
Asali: UGC

Shugaban APC na Akwa Ibom, Stephen Ntukekpo, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana wasiƙar da mashahuriyar ƙarya da wasu tsirarun mutane suka kirkira don jan hankalin al'umma.

Kara karanta wannan

'APC Ta Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya Wanda Ka Iya Shafar Su Tinubu a 2023'

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina mai tabbatar da cewa bamu taɓa tunani ko ɗakatar da Honorabul Minista ba a matakin gunduma ko jiha. Muna kira ha ɗaukacin al'umma da mambobin jam'iyar mu su shure batun domin ƙaryace da kokarin yaɗa fasadi."

Mista Ntukekpo ya ayyana Ministan da cikakken ɗan jam'iyya mai goyon bayan haɗin kan jam'iyyar APC a Akwa Ibom.

"Ina rokon mambobin jam'iyyarmu da su maida hankali kan harkokin yakin neman zabe, su bar kula irin waɗan nan karerayin," inji shi.

Haka zalika shugabannin APC a gundumar Umana watau Ndiya, ƙaramar hukumar Nsit Ubium sun fitar da makamanciyar wannan sanarwa ta karyata labarin.

Wasikar dakatarwa ta bogin ta bayyana ne a daidai lokacin da APC ta kori Mista Ita Enang, tsohon mai baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari shawara.

Shugaban APC na jihar, Mista Ntukekpo, yace sun kori Enang ne saboda ƙarar da ya shigar da jam'iyya gaban Kotu kan burinsa na takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Kamfe Saboda Babban Rashi Da Ta Yi A Imo

'APC Ta Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya Wanda Ka Iya Shafar Su Tinubu a 2023'

A wani labariin kuma Sakataren tsare-tsare na APC a jihar Adamawa ya ce sauya Shekar tsohon gwamna Jibrilla Bindow babban rashi ne

Mustapha Atiku Ribadu yace duk da ga aikata kuskure a zamanin mulkinsa amma Bindow yana da matuƙar tasiri a siyasa idan aka duba abu 2.

Sai dai duk da haka jigon siyasan ya bayyana cewa APC ce zata samu nasara a jihar Adamawa duk da wannan babban rashin kuma suna aiki ba dare ba rana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel