Canjin Kuɗi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ziyarar da Shugaba Buhari Zai Kawo Jihar

Canjin Kuɗi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ziyarar da Shugaba Buhari Zai Kawo Jihar

  • Gwamnatin Kano ta ɗage ziyarar da shugaban ƙasa Buhari zai kawo Kano domin kaddamar da ayyuka
  • A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta bayyana manyan dalilin da ta hanga ya sa ta ɗauki wannan matakin
  • Shugaba Buhari zai kai ziyara don kaddamar da wasu ayyukan Ganduje a Kano tsakanin 30 da 31 ga watan Janairu kafin wannan ci gaban

Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Asabar, ya rubuta wasika ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana neman ya ɗage ziyarar da zai kawo jahar.

Ganduje yace ya nemi haka ne bayan korafin da Kanawa suka yi kan wahalar da suke sha wajen samun sabbin takardun kuɗi, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Gwamna Ganduje.
Canjin Kuɗi: Gwamnatin Kano Ta Dage Ziyarar da Shugaba Buhari Zai Kawo Jihar Hoto: premiumtimes
Asali: Twitter

Gwamnan yace yan majalisun Kano, shugabannin siyasa da 'yan kasuwa sun goyi bayan matakin ɗage zuwan shugaban ƙasa, ya kuma roki a ƙara wa'adin daina karban tsaffin kuɗi.

Kara karanta wannan

2023: Rigima Ta Kara Ɓarkewa a PDP Bayan Su Wike, An Dakatar da Shugaban Jam'iyya na Wata Jiha

A wata sanarwa da hadimin Ganduje, Abba Anwar ya fitar ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda wahalar da mutane ke ciki sakamakon ƙarancin wa'adin dena amfani da tsaffin kuɗi na babban bankin CBN, Ganduje ya bayyana cewa Kano ta rubuta wasika zuwa fadar shugaban kasa."
"Wasikar ta nemi a ɗage ziyarar da shugaban ƙasa kai kawo jihar Kano domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka."

Sanarwan ta kara da cewa an cimma matsayar daukar wannan matakin ne ranar Jumu'a a gidan gwamnati yayin ganawa da Malamai, 'yan majalisu, shugabannin siyasa da yan kasuwa.

"An ɗauki wannan matakin ne domin gujewa faruwar wani abu da ba'a yi tsammani ba," a cewar Sanarwan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa kafin wannan ci gaban, an tsara zuwan shugaban kasan ne a tsakanin Ranakun 30 da 31 ga watan Janairu, 2023 domin ya kaddamar da wasu ayyukan Ganduje.

Kara karanta wannan

Canjin Takardun Kudi: Kira Zuwa Ga Hukuma, Daga Dr Sani Rijiyar Lemo

"Yayin da muke dakon wannan ziyara mun tsinci kanmu a tsaka mai wuya, wanda ya jefa mutanen mu cikim wahala. Dogaro da dalilan tsaro mun nemi shugaban ƙasa ya ɗage ziyarar."

- Ganduje.

First Bank da GT Sun Amince Zasu Yi Aiki A Karshen Mako Don Karban Tsaffin Kudi

A wani labarin kuma Manyan Bankuna 2 sun bayyana cewa zasu buɗe a ranakun karshen mako domin su karbi tsaffin kuɗi

A ranar 31 ga watan Janairu, 2023 nan da kwanaki kaɗan tsoffin takardun N200, N500 da N1000 zasu daina amfani.

A wata sanarwa da mahukuntan bankunan suka fitar ranar Jumu'a, sun bayyana cewa sun tsara aiki a karshen mako ne don mutane su samu damar shigar da tsoffin kuɗinsu kaɗai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel