INEC Ta Jefa NNPP Cikin Matsala, Zabe Ya Karaso, Jam’iyyar ba ta da ‘Yan Takara

INEC Ta Jefa NNPP Cikin Matsala, Zabe Ya Karaso, Jam’iyyar ba ta da ‘Yan Takara

  • Jam’iyyar NNPP ta zargi Hukumar INEC da kin bin hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yi
  • Sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP ya zargi INEC da biyewa siyasa a maimakon bin doka
  • Dr. Agbo Major ya ce hukumar zaben kasar ta ki karbar wasu canje-canjen ‘yan takara da suka yi

Abuja - Jam’iyyar NNPP ta ce kin karbar ‘yan takaransu da hukumar INEC tayi duk da umarnin da kotu ta yi, ya nuna akwai siyasa a lamarin na ta.

Daily Trust ta ce INEC ta ki bin umarnin babban kotu na canza masu neman takara a NNPP a 2023.

Sakataren yada labaran NNPP na kasa, Dr. Agbo Major ya kira taron manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke garin Abuja, ya koka a kan batun.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Kwankwaso Ya Yi Alkwarin Gyara ‘Kuskuren’ da Aka Yi Idan Ya Ci Zabe

Dr. Agbo Major yake cewa kin maye gurbin ‘yan takaran da suka sauya-sheka ko su kayi murabus daga jam’iyyar ya nuna INEC ta sabawa dokar kasa.

Doka ba ta aiki a Najeriya?

Kakakin na NNPP yake cewa idan har abubuwa su na tafiya daidai, ana bin doka, babu yadda hukumar zabe ta sabawa umarnin kotun daukaka kara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai magana da yawun jam’iyyar ya ce sun kai wa hukumar zaben canjin sunayen ‘yan takara a karshen Agustan 2022 da kuma cikin Satumban 2022.

NNPP.
Magoya bayan NNPP a Kano Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

'Yan takaran da abin ya shafa

Jaridar This Day ta ce ‘yan takaran da aka ki canzawa NNPP sun hada da Sanata Rufai Hanga a madadin Sanata Ibrahim Shekaru a Kano ta tsakiya.

Shekarau ya samu takarar kujerar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, amma daga baya ya hakura da tikitin, sai ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Kamfe Ya Tsaya Babu Shiri Bayan An Kora ‘Yar Takarar M/Gwamna da Ta je Yakin zabe

NNPP na so Murtala Garba ya canji Hon. Ibrahim Mikra a Taraba, Zakari Yau Hassan a madadin Mohammed Seidu Maikifi a kujerar majalisar jihar Yobe.

An fahimci jam’iyyar NNPP tana ikirarin Kotun daukaka ta amince mata canza sunayen wadanda aka ba takara da farko, ta maye gurbinsu da wasu.

Jam’iyyar hamayya ta NNPP take cewa abin takaici ne a maimakon hukumar da aka sani da tsare damukaradiyya ta yi abin da ya dace, sai tayi watsi da doka.

An kai Funke Akindele kotu

Wani rahoto mara dadi da aka fitar a baya, ya nuna yadda wasu miyagu suka hana ‘yar takarar Mataimakiyar Gwamna a PDP yin kamfe a kasuwar Legas.

Shahararriyar ‘yar wasar fim, Funke Akindele da ke neman mulki a Jam’iyyar PDP ta ji babu dadi da ta shiga kasuwar nan ta Ikosi da ake saida kayan marmari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng