Zaben 2023: Peter Obi Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Zaben 2023: Peter Obi Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

  • Batutuwa na ta kara warwarewa yayin da shirin zaben shugaban kasa da za a gudabar ranar Asabar 25 ga wata mai kamawa na Fabrairu
  • Akwai batun da yake yawo wanda yake tabbatar da cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi zai janye daga takarar
  • Yayin mayar da martani, jam'iyyar ta Labour Party tace jita-jita ne kuma karya ce kuma Obi na kan gaba don yin nasara a zaben mai zuwa

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Obi-Datti ya karyata batun janyewar Peter Obi daga takarar a watan mai kamawa.

A bayanan kwamitin na Obi-Datti, ya bayyana cewa batun janye takara tare da hadin gwiwa da dan takarar PDP Atiku Abubakar ba gaskiya bane.

Peter Obi, Labour Party
Zaben 2023: Peter Obi Ya Janye Daga Takarar Shugaban Kasa? Gaskiya Ta Bayyana. Hoto: Labour Party
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan Takarar Shugaban Kasa Sun Bayyana Abinda Zasuyi A Kwana 100 Farko

Jam'iyyar ta bayyana hakan a matsayin abin haushi da kuma karya tare da bayyana cewa Obi ne sahun gaba don lashe zaben ya kuma ceto kasarnan daga halin da take ciki.

Jam'iyyar LP tayi kakkausan martani a wata sanarwa da ta fitar, jam'iyyar ta ce:

''Ba abin takaici kamar ace mutum 18 na gasar tsere don cin kofi kuma wani ya dinga tunanin wanda yake kan gaba kuma ya fara hango kofi da ya janye wa wani da yake baya.
''A bayyana yake yadda sauran jam'iyyu da suke takarar suke tsokanar dan takarar LP a kyautukan cin hanci da kamar buhun shinkafa, fastoci da kuma allunan talla ya nuna yadda tasirin wanda suke son kayarwa a wannan tseren.''

Jam'iyyar ta shaida cewa takarar Obi ta zama abin sanya ido daga sassan duniya da kuma sauran masu ruwa da tsaki a cikin kasarnan.

Kamar yadda rahoton Nigerian Tribune ya shaida:

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi

''Maganar gaskiya shine yanzu ana gwada sauran yan takarar ne da irin nagartar Peter Obi.''

Peter Obi zai shiga zabe a matsayin dan takara sahun farko da yake da yiwuwar lashe zabe kamar yadda aka dinga bayyanawa tun farko a zaben na wata mai kamawa.

Obi zai fafata da manyan yan takara kamar Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki da kuma Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Takalman da Peter Obi ya saka zuwa yakin neman zabe sun janyo cece-kuce a Imo

Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Mr Peter Obi ya nuna kankan da kai ta hanyar irin tufa da takalmi da ya ke saka wa zuwa kamfen.

Yanayin shigar da Obi ya yi wurin taron kamfen din sa a Owerri, babban birnin jihar Imo ya dauki hankulan al'umma musamman a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel