Atiku Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Fallasa ‘Mugun Shirin’ da Tinubu Yake Kullawa

Atiku Ya Ankarar da ‘Yan Najeriya, Ya Fallasa ‘Mugun Shirin’ da Tinubu Yake Kullawa

  • Atiku Abubakar yana tuhumar Asiwaju Bola Tinubu da yunkurin kawo juyin-juya-hali a Najeriya
  • ‘Dan takaran na jam’iyyar PDP ya ce bai kamata ayi wasa da kalaman da Tinubu ya yi a Ogun ba
  • Wazirin Adamawa ya ce ‘dan takaran ya taba makamantan wadannan kalamai a birnin Abeokuta

Abuja - Atiku Abubakar mai neman mulkin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, yana zargin Asiwaju Ahmed Tinubu na APC da kokarin kawo juyin-juya-hali.

A wani jawabin Phrank Shaibu da Vanguard ta gani, an ji ‘dan takaran jam’iyyar PDP ya zargi abokin gwabzawarsa a zabe da nufin jawo rigingimu a Najeriya.

Mista Phrank Shaibu wanda shi ne Mai ba Atiku Abubakar shawara na musamman a kan hulda da jama’a yake cewa APC na nufin tada zaune tsaye a 2023.

Kara karanta wannan

Katon Kuskure ne Zaben Atiku Abubakar Inji Tsohon Hadiminsa da Ya Tona Masa Asiri

A jawabin da ya fitar a ranar Alhamis, Hadimin ‘dan takaran ya ce babatun da Bola Ahmed Tinubu ya yi a wajen taron yakin zabe a Abeokuta ya fallasa shi.

Magana ta fara fitowa - Shaibu

Phrank Shaibu yake cewa kalaman da ‘dan takaran ya yi a jihar Ogun somin-tabin shirinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin Shaibu, ya tunawa ‘Yan Najeriya haka uban gidan ‘yan siyasan na Legas ya yi irin wadannan kalamai da ya kai ziyara zuwa Abeokuta a bara.

Tinubu
Bola Tinubu wajen kamfe Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

A lokacin, saura kwanaki 29 a shirya zaben ‘dan takara, Shaibu ya ce amma Tinubu ya rika magana tamkar wanda ya ci zabe, yana yi wa APC barazana.

Rahoton da aka fitar ya kara da cewa da yake jawabi a birnin Abeokuta, Atiku ya ce Tinubu ya fada da yarbanci cewa juyin juya-hali za ayi a zaben bana.

Kara karanta wannan

An Kai wa Tawagar ‘Dan Takarar Shugaban Kasa Hari Sau 2 Wajen Yawon Kamfe

Wannan juyin juya-hali ne. Zaben nan juyin juya-hali ne. Ba su so mu samu kuri’u, suna so su birkita lamarin. Kun yarda?
Zan kawo juyin juya-hali.” - Bola Tinubu

Anya kuwa... - Atiku Abubakar

“Irin wadannan maganganu ba suyi kama da na wanda zai yarda ya sha kashi idan har ya rasa zaben shugaban kasar da zai shiga ba.
Bola Tinubu bai fi karfin dokar kasa ba, kuma bai gagari jami’an DSS ko dakarun ‘yan sanda su titsiye shi domin su bincike shi ba.
Domin gujewa zubar da jini a zabe mai zuwa, ka da ayi wasa da kalaman ‘dan takara, juyin-juya-hali yana nufin kifar da gwamnati.

CUPP tana tare da Atiku/Okowa

Rahoto ya zo cewa gamayyar Jam’iyyun siyasa a jihohin Kudancin Najeriya sun tsaida ‘dan takaransu tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Kungiyar CUPP ta ce ganin Atiku na goyon bayan a canza fasalin kasa, kuma ya yi mataimakin shugaban kasa, sannan ya dauko Kiristan Ibo, za su bi bayansa.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu Ya Shawo Kan Gwamnonin APC, Aka Ba Shi Takara - Najaatu Mohammed

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng