Peter Obi Ya Kai Ziyarar Bazata Kudancin Borno, Ya Kafa Tarihi
- Mr Peter Obi ya kai ziyara mai tarihi zuwa kudancin Borno a matsayin wani sashi na kamfen dinsa
- Jami'an jam'iyyar Labour sun ce wannan shine ziyara ta farko da dan takarar shugaban kasar ya kai yankin da ta'addanci ya yi wa illa
- Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya samu tarba mai kyau daga mutanen yankin da suka fito domin su gan shi
FCT, Abuja - A cikin wani sashi na yakin neman zabe don zama shugaban Najeriya na gaba, Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour (LP), ya kai ziyarar bazata masarautar Biu, kudancin jihar Borno.
Jami'an jam'iyyar Labour sun ce wannan shine karo na farko da dan takarar shugaban kasar ya kai yankin da ta'addanci ya yi barna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hotuna da bidiyo da magoya bayan jam'iyyar Labour suka wallafa a dandalin sada zumunta ya nuna yadda mutanen yankin kudancin Borno ke murna lokacin da suka ga Obi.
A jawabinsa da Olusegun Dosunmu ya aike wa Legit.ng, Obi ya yi alkawarin kawar da wahalhalu da share hawayen mutanen kudancin Borno.
An ambato yana cewa:
"Ina daya cikinku kuma na san halin da kuke ciki. Na san ku ba ragwaye bane kuma kuna son komawa gonakun ku. Ina muku alkawari cewa rashin tsaro ba zai zama tarihi kuma zan tabbatar gwamnati na ta baku rayuwa mafi kyau."
Obi yana tare da abokin takararsa, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed, shugaban jam'iyyar LP na kasa, Julius Abure; dan takarar gwamna na jihar Borno, Kyaftin Ibrahim Mshelia wanda shine jagoran shirya taron kuma mataimakin manajan kamfen na kasa, Isaac Balami da wasu.
A jawabinsa, Kyaftin Mshelia wanda dan asalin karamar hukumar Hawul ne da ke kudancin Borno ya bawa mutanen da suka halarci taron tabbacin cewa idan an zabe shi gwamna da Obi a matsayin shugaban kasa, za a dawo da tsaro da harkokin kasuwanci jihar Borno, kuma abubuwa za su habbaka.
Ya kammala da cewa a matsayinsa na dan jihar, ba zai bawa mutanen kunyan Borno kunya ba.
A bangarensa, Balami, wanda shine babban mashawarci kan harkokin kamfen na shugaban kasa, samar da kudi da tattaro kan mutanen karkara ga shugaban jam'iyyar LP na kasa, ya ce ya yi farin cikin ganin yan Najeriya na kokarin ganin nasarar Obi/Datti.
IBB ya karyata cewa yana goyon bayan Peter Obi
Kun ji cewa Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban kasa na mulkin soja ya karyata jita-jitar cewa ya mara wa Peter Obi na jam'iyyar LP baya.
Kakakin IBB, Kassim Afegbua ya karyata rahoton a wani rubutu da ya yi a Twitter, yana mai cewa mai gidansa ba shi da wani dan takara na kansa a zaben na 2023.
Asali: Legit.ng