Zan Rufe Dukkan Sansanonin Yan Gudun Hijira Idan Na Zama Shugaban Kasa, Buhari

Zan Rufe Dukkan Sansanonin Yan Gudun Hijira Idan Na Zama Shugaban Kasa, Buhari

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗaukarwa yan gudun Hijira alƙawari a ralin APC na Benuwai
  • Ɗan takarar shugaban kasan ya ce idan ya kai ga nasara zai kulle sansanonin yan gudun Hijira ya maida mutane garuruwansu
  • Tinubu ya jaddada kudirinsa na gyra bangaren ilimi da kuma baiwa Ɗaliban jami'oi bashi

Benue - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatarwa yan gudun hijira a jihar Benuwai cewa zasu koma gidajensu da zaran ya ci zaɓe.

Tinubu ya yi wannan alƙawarin ne yayin da yake jawabi ga dubun dubatar magoya bayan APC a wurin Ralin kamfen shugaban kasa da ya gudana a filin wasan Aper Aku, Makurdi.

Bola Tinubu a Benuwai.
Zan Rufe Dukkan Sansanonin Yan Gudun Hijira Idan Na Zama Shugaban Kasa, Buhari Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ya ce babu dalilin da zai sa mutane su ci gaba da zama matsugunan 'yan gudun Hijira a ƙasarsu ta gado, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ya fasa kwai: Tinubu ya fadi makarkashin yin sabbin Naira da karancin mai a Najeriya

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Matukar kuka zaɓe ni zan kulle dukkan sansanonin yan gudun Hijira sannan zan maida mutanen da suka rasa mahallansu garuruwansu na basu fata nagari."
"Biyan Albashin ma'aikata ba zai ƙare ba, za'a samu hasken wutar lantarki ba ɗauke wa kuma zamu kara ingancin Ilimi a ƙasar nan ciki harda baiwa ɗalibai rance."

Bayan nan ɗan takarar shugaban ƙasan ya tuna kyakkyawar alaƙa da ta daɗe tsakaninsa da Ministan harkokin gwamnati da ayyuka na musamman, George Akume.

Tinubu ya bayyana Sanata Akume da mutum mai gaskiya kuma ɗan siyasan abin dogaro.

Tinubu ya aika sako ga Atiku?

Ɗan takarar ya kuma kalubalanci abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya fito ya bayyana tushen inda yake tara dukiyarsa.

A cewar tsohon gwamnan mutane ba zasu gamsu ba idan yace ya taba aikin Kwastam da wani kamfanin tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Yan Arewa Sun Lalubo Mafita, Sun Bayyana Abinda Zasu Koma Amfani da Shi Saboda Rashin Sabbin Kuɗi

Bugu da ƙari, Tinubu ya bayyana ɗan takarar gwamnan APC a jihar Benuwai, Hycinth Alia a matsayin fata ga mutanen jihar, ya roki mazauna su kaɗa masa kuri'a.

A wani labarin kuma APC Ta Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya Wanda Ka Iya Shafar Su Tinubu a 2023

Sakataren tsare-tsare na jam'iyyar APC reshen jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, ya bayyana cewa sauya sheƙar tsohon gwamna, Jibrilla Bindow, babbar matsala ce ga APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel