Yan Kasuwan Sakkwato Sun Bullo da Mafita Saboda Karancin Sabbin Kudi

Yan Kasuwan Sakkwato Sun Bullo da Mafita Saboda Karancin Sabbin Kudi

  • Shugabannin 'yan kasuwa a jihar Sakkwato sun fara kokarin shawo kan rashin sabbin takardun kuɗi a hannun jama'a
  • 'Yan kasuwan sun gana da jami'an babban bankin ƙasa CBN a wani yunkurin nemo mafita don kada kasuwanci ya tsaya
  • Kwanturolan CBN na Sakkwato yace sun ɗauki matakin da ya dace domin sabbin kuɗi su isa hannun mutane

Sokoto - A wani yunkurin rage raɗaɗin karancin sabbin takardun kuɗi a hannun jama'a, shugabannin ƙungiyar 'yan kasuwan jihar Sakkwato sun amince da amfani da E-Naira a harkokin kasuwancinsu.

Da yake jawabi a madadin Ƙungiyar, Alhaji Yaro Gobirawa, ya ce zai haɗa kan mambobin su rungumi tsarin mu'amalar kuɗi ta asusun banki domin rage yawan takardun kuɗin dake yawo.

Yan kasuwan Sakkwato.
Yan Kasuwan Sakkwato Sun Bullo da Mafita Saboda Karancin Sabbin Kudi Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridar Punch tace Gobirawa ya yi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan ganawa da ma'aikatan babban bankin Najeriya (CBN) ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Sokoto: Jama'a Sun Rude Bayan 'yan Kasuwa Sun Daina Karbar Tsofaffin Kudi

Ya bayyana cewa mambobin ƙungiyar 'yan kasuwa na jihar Sakkwato a shirye suke su fara mu'amalar kuɗi ta manhajar E-Naira a matsayin hanyar tafiyar da kasuwancinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Goburawa ya kuma yi kira ga CBN ya umarci Bankunan 'yan kasuwa masu rassa a jihar Sakkwato su samar da isassun ma'aikatan da zasu riƙa sauraron bukatun 'yan kasuwa.

Haka zakila ya roki jagororin CBN da su yi duk me yuwuwa wajen tabbatar da sabbin kuɗi sun wadata domin rage wahalhalun da yanzu haka mutane ke fama da su.

CBN ta kirkiro tsarin musaya

Tun da farko, kwanturolan CBN na jihar Sakkwato, Dahiru Usman, ya yaba wa 'yan kasuwan bisa kokarinsu na baiwa bankin haɗin kai a kowane lokaci.

Kwanturolan ya tabbatar da cewa CBN zai tura wasu daga cikin ma'aikatan sashin fasaha zuwa kasuwanni domin taimakawa mutane su san yadda ake amfani da manhajar E-Naira.

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: CBN Ta Faɗi Abu 2 da Sabbin Kudi Suka Yi Wa Yan Bindiga Da Sabon Tsari Ga Yan Ƙauye

Bugu da Kari, Usman ya bayyana cewa babban bankin ƙasa ya kawo sabon tsarin musaya, wanda kowane ɗan Najeriya zai iya sauya tsoffin kuɗi da sabbi daga N10,000 zuwa ƙasa.

A cewarsa, wannan zai rage wa mutane wahalhalun da suke fama da su yanzu haka sakamakon sauya takardun Naira, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Sabbin Kudi sun rage yawan sace mutane da neman kuɗin fansa, CBN

A wani labarin kuma Gwamnan CBN yace a iya tunaninsa tsarin sauya takardun naira ya rage yawacn garkuwa da mutane da neman fansa

Godwin Emefiele ya ce duk da ba dole tunaninsa ya zama gaskiya ba amma yana ganin wannan sauya kudin zai taimaka wa yankunan da ba zaman lafiya.

Bayan haka, Gwamnan ya bayyana tsarin da suka shirya wa talakawa da masu karamin ƙarfi domin sabbin kudin su isa garesu ko da bayan wa'adi ya cika.

Asali: Legit.ng

Online view pixel