Zaben 2023: Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar Accord Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ya Zargi PDP

Zaben 2023: Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar Accord Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ya Zargi PDP

  • An zargi jam'iyyar Peoples Democratic Party a jihar Ribas da yunkurin kashe wani dan takarar gwamna
  • Dumo Lulu-Briggs, dan takarar gwamnan jam'iyyar Accord a jihar Ribas ya zargi PDP da yin barazana ga rayuwarsa
  • Lulu-Briggs ya ce shugabancin jam'iyyar Accord ya samu rahoton cewa wasu da ake zargin guggun yan PDP ne sun kai hari sakatariyarsu kafin aka far masa a hanyar zuwa wajen

Dan takarar gwamnan jam'iyyar Accord a jihar Ribas, Dumo Lulu-Briggs, ya yi gagarumin zargi a kan shugabancin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ribas.

Da yake magana kan yadda ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar, 21 ga watan Janairu, yayin wata ziyara da ya kai karamar hukumar Etche ta jihar, Lulu-Briggs, ya yi zargin cewa PDP na barazana ga rayuwarsa a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ɗaya Kafin Zabe, Atiku da PDP Sun Samu Gagarumar Nasara a Jihar Tinubu

Dan takarar gwamnan jam'iyyar Accord a jihar Ribas
Zaben 2023: Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar Accord Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Ya Zargi PDP Hoto: Dumo Lulu-Briggs
Asali: UGC

Ainahin abun da ya faru

Yayin da dan takarar gwamnan da tawagarsa suka je karamar hukumar don tabbatar da rahotannin harin da aka kai sakatariyar jam'iyyar Accord a yankin, wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun farmaki ayarin motocinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Motarsa wanda harbin bindiga baya shiga ya cika da shaidar hasasai, yayin da ya yi nasarar fita daga yankin da taimakon jami'an tsaro, jaridar Punch ta rahoto.

PDP ce ke da alhakin harin da aka kai mani, inji Lulu-Briggs

Lulu-Briggs ya kuma tabbatar da harin yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce an sanar da shi cewa an kai farmaki sakatariyar jam'iyyar da ke Igbo-Etche, karamar hukumar Etche, wanda ya sa shi kai ziyara chan, rahoton PM News.

Ya bayyana cewa yayin da yake hanyarsa ta zuwa, miyagun sun bude masa wuta sannan suka yi wa ayarinsa ruwan harsasai.

Kara karanta wannan

Makiyan Jihar Bauchi Ne Kadai Za Su Zabi Dan Takararmu, Inji jiga-Jigan APC Da Suka Sauya Sheka Zuwa PDP

Ya ce:

"Mun samu rahoto mai cike da damuwa cewa wasu guggun mutane da PDP ta shirya sun kai hari sakatariyar jam'iyyarmu.
“Saboda haka dole mu je mu ga abun da ke wakana a sakatariyarmu. A hanyarmu ta zuwa chan, wadannan mutanen suka kuma bude mana wuta.
"Sun farmake mu, sun lalata motocinmu, sun harbi motata. Kuna iya ganin motata, dukkanin gilashen motar sun ruguje."

A wani labarin kuma, Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya ce kada iyayen yara su damu domin da zaran ya lashe zabe za su daina tunanin mai za su ba 'ya'yansu su ci don abinci zai yalwata a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel