Buhari Zai Ziyarci Kano Mako Na Gaba, Zai Kaddamar da Manyan Ayyuka

Buhari Zai Ziyarci Kano Mako Na Gaba, Zai Kaddamar da Manyan Ayyuka

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Kano a mako mai zuwa na tsawon kwanaki biyu kamar yadda kwamshinan yada labaran jihar ya sanar
  • Buhari wanda zai je Kano a ranar Litinin 30 zuwa 31 ga watan Janairu, zai kaddamar da muhimman ayyukan da Gwamna Ganduje yayi a jihar
  • Zai kaddamar da wutar lantarki mai zaman kanta ta jihar, aikin Dam don Tiga, cibiyar koyar da sana’a ta Dangote da sauransu duk a cikin kwanakin biyu

Kano - Shugaba Muhammad Buhari zai kaddamar da aikin wutar lantarki mai zaman kanta ta jihar Kano a ziyarar kwana biyu da zai kai jihar daga 30 zuwa 31 ga watan Janairun 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Baba Buhari
Buhari Zai Ziyarci Kano Mako Na Gaba, Zai Kaddamar da Manyan Ayyuka. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kwamishinan yada labari na jihar kuma kakakin gwamnan, Muhammad Garba, ya bayyana hakan yayin jawabi ga manema labarai kan kokarin kwamitin wurin tabbatar da nasarar APC a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Bayan Gazawar APC da PDP, Yan Najeriya Suna da Wani Zabi Ɗaya Rak

Hakazalika, Garba ya bayyana cewa a yayin ziyarar kwanaki biyun da zai kai, zai kaddamar da ayyuka a cibiyar koyar da ayyukan dogara da kai ta Dangote, Dala Inland Port, rukunin gidajen malamai na karamar hukumar Ungogo, aikin wutar lantarki mai zaman kansa, Tiga Dam da gadar Muhammadu Buhari.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Megawatts 10 na wutar lantarkin za su dinga ba wa fitillun kan tituna, masana’antu, ayyukan wutar lantarki da sauran muhimman bangarori.

A yayin jawabi kan zaben, Garba ya bayyana tabbacinsa da kwarin guiwa kan cewa ‘dan takarar gwamnan jihar na APC ne zai lashe zaben.

A yayin sharhi kan zaben da ba a kammala ba, Garba yace lamari ne da ya shafi kundin tsarin mulki inda ya kara da cewa za a kare faruwar hakan a 2023 kamar yadda yace APC za ta kare kuri’unta a zabukan.

Kara karanta wannan

Kaico: An kama kuturu da makaho da ke harkallar miyagun kwayoyi a Najerjiya

Jigawa: 'Yan PDP sun share wurin da Tinubu yayi kamfen

A wani labari na daban, magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Jigawa, sun yi gangami tare da share filin wasan da Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na APC, yayi amfani da shi a jihar.

A cewarsu, sun share rashin tsaro, fatara da jinin jama;a da aka zubar a jihar duk a karkashin mulkin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel