Tinubu Musulmin Boge Ne, Yan Arewa Ba Zasu Zabeshi Ba: PDP

Tinubu Musulmin Boge Ne, Yan Arewa Ba Zasu Zabeshi Ba: PDP

  • Ana cigaba da musayar yawu tsakanin kwamitocin kamfen manyan jam'iyyun siyasan Najeriya biyu
  • Yayinda Jam'iyyar APC tayi kira ga hukumomin tsaro su damke Atiku kan rashawa, PDP ta ce a kama Tinubu saboda zargin ta'amuni da kwaya
  • Yanzu kuma kakakin kamfen Atiku ya ce Tinubu ba musulmin gaskiya bane, na bogi ne

Kwamitin kamfen kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya ce yan arewa ba zasu zabi Musulmin boge ba, wanda ke kokarin yaudarar mutane da tikitin Musulmi da Musulmi.

Diraktan sadarwa na kwamitin kamfen, Dele Momodu, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar jiya, rahoton Thisday.

Ya bayyana cewa ko kadan yan Najeriya ba zasu yaudaru da tikitin Musulmi da Musulmi da APC tayi ba.

Atiku
Tinubu Musulmin Boge Ne, Yan Arewa Ba Zasu Zabeshi Ba: PDP
Asali: Twitter

Dele Momodu ya bayyana cewa dan takarar PDP, Atiku Abubakar, zai lashe kuri'un Arewa maso gabas, Arewa maso yamma, Arewa maso tsakiya da kudu maso kudu, yayinda Tinubu ya samu wasu tsirarun jihohi a Arewa da kudu maso yamma.

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Faɗi Sunayen Jihohin Da Atiku Zai Sha Kaye a Zabe Da Dalilai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce babu jihar da Atiku ba zai samu rubu'in kuri'u ba.

A cewarsa:

"Ban san wata jiha da PDP ba zata samu 25% na kuri'u ba kuma daga bisani ta lashe zaben. An raba kan Najeriya yanzu sosai kuma mutane zasu yi zabe ne bisa kabilanci."
"Yan arewa ba zasu zabi "Musulmin Boge" ba da sunan Muslim/Muslim ticket. Yan Najeriya tuni sun gane wannan yaudara."

Momodu ya cigaba da cewa yankin Arewa maso gabas ba zasu so su rasa samun shugaban kasa ba karo na farko tun bayan mutuwan Tafawa Balewa.

A riwayar Guardian, yace:

"Arewa maso gabas ba zasu zabi matsayin mataimakin shugaban kasa yayinda rabonsu da kujerar shugaban kasa tun 1966."
"Hakazalika yan arewa maso yamma ba zasu taba watsi da Atiku su zabi Tinubu ba."
"Ina hasashen cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ne zai zama shugaban kasa Najeriya."

Kara karanta wannan

Damammakin da manyan yan takarar shugaban kasa 4 ke da shi a jihohi 5 mafi yawan kuri'u

Bola Tinubu bai samun goyon bayan da ake sa rai daga wajen Buhari Inji Jigon APC

Tsohon dan takarar gwamnan Legas zamanin CPC kuma jigon jam'iyyar APC, Abayomi Mumuni, ya ce Buhari na munafuntar Bola Tinubu.

Abayomi Mumuni ya ce Buhari bai nuna goyon baya ga Tinubu kamar yadda aka yi tsammani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel