Abin Da Yasa Ba A Ganin Osinbajo Wurin Kamfen Din Tinubu, APC

Abin Da Yasa Ba A Ganin Osinbajo Wurin Kamfen Din Tinubu, APC

  • Daga karshe, jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta bayyana dalilin da yasa Osinbajo baya zuwa kamfen din Bola Tinubu
  • Festus Keyamo, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC ya ce Shugaba Buhari ne ya ce Tinubu ya maya da hankali wurin aikin gwamnati
  • Keyamo ya ce jam'iyyar ta APC kan ta hade ya ke wuri guda ba kamar jam'iyyar PDP da ke hanyar rushewa ba saboda rashin jituwa

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta bayyana dalilin da yasa ba a ganin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wurin kamfen din dan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu.

Tun bayan kaddamar da kamfen din Tinubu a Jos a ranar 15 ga watan Nuwamban 2022, ba a taba ganin wasu mambobin APC ciki har da mataimakin shugaban kasar na yi wa dan takarar jam'iyyar kamfen ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

Osinbajo
Abin Da Yasa Ba A Ganin Osinbajo Wurin Kamfen Din Tinubu, APC. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana ganin Osinbajo yana halartar wasu tarruka, ciki har da bikin cikar makarantar Baptist High School shekaru 100 a baya-bayan nan a Abeokuta, amma bai ce uffan ba kan kamfen din Tinubu tun bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwani.

Ko a kafafen sada zumunta inda mataimakin shugaban kasar ke da mabiya, ba a ga yana wallafa abubuwa masu alaka da kamfen din ba don nuna goyon bayan takarar Tinubu.

Kazalika, shima ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ba a gan shi a kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar.

Shugaba Buhari ne ya umurci Osinbajo ya mayar da hankali kan aikinsa - Keyamo

Da ya ke martani, kakakin kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa na APC, Festus Keyamo, ya ce mataimakin shugaban kasar na biyayya ga umurnin Shugaba Muhammadu Buhari ne na mayar da hankali kan aikinsa na gwamnati.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Ya ce:

"Rotimi Amaechi (tsohon ministan sufuri) ya halarci kamfen a Adamawa da Jos; ya ce yana zuwa ralli amma sai wanda ya zaba.
"Shi kuma mataimakin shugaban kasa, umurni aka bashi ya mayar da hankali kan aikin gwamnati kuma kana iya gani Shugaban Kasa yana zuwa kamfen. Shi kuma Ngige ba ya adawa da jam'iyyarmu, ya zabi ya kada ya yi wa kowa kamfen kuma minista daya ne cikin 43.
"Muna da hadin kai mai karfi a APC akasin PDP da ta kusa rushe wa."

Jam'iyyar PDP ta dakatar da Sanata Chimaroke Nnamani da ke goyon bayan Tinubu

Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta dakatar da Chimaroke Nnamani, sanata mai wakiltar Enugu East a majalisa.

Mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Debo Ologunaba ne ya bayyana hakan cikin wata takarda da ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel