Arewa Ba Za Ta Bi Addini Ba Wajen Zabe a 2023, Inji APC

Arewa Ba Za Ta Bi Addini Ba Wajen Zabe a 2023, Inji APC

  • Jam'iyyar APC ta yi martani ga furucin PDP kan tikitin Musulmi da Musulmi, tana mai cewa yankin arewa ba za ta yi zabe kan addini ba a 2023
  • Dele Momodu, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya yi ikirarin cewa arewa ba za ta zabi Musulmin bogi ba da sunan tikitin Musulmi da Musulmi
  • A martaninsa Bala Ibrahim, daraktan labaran APC, ya bayyana Momodu a matsayin dalibin tarihi da ya gaza, yana mai cewa arewa bata la'akari da addini wajen zabe

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da batun cewa arewacin Najeriya wacce ke da 50% na masu rijistan zabe a 2023, suna zabe bisa la'akari da addini.

Yan Najeriya za su fito kwansu da kwarkwatarsu a yan makonni masu zuwa domin zaben dan takarar shugaban kasar da suke so ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu Musulmin Boge Ne, Yan Arewa Ba Zasu Zabeshi Ba: PDP

Yan takarar shugaban kasa
Arewa Ba Za Ta Bi Addini Ba Wajen Zabe a 2023, Inji APC Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Halin da ake ciki game da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Kwankwaso, PDP, APC da zaben 2023

Masana siyasa sun ce zaben ya kasance tsakanin Bola Tinubu na APC, Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na Labour Party da Rabiu Kwankwaso na NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana game da zabe mai zuwa, Dele Momodu, daraktan labarai na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya ce arewa ba za ta zabi "musulmin bogi" ba yayin da ya ke hasashen nasarar Atiku.

Yadda arew za ta yi zabe a 2023

Yayin da yake martani ga ikirarin Momodu, Bala Ibrahim, daraktan labaran APC, ya bayyana masu wannan tunanin na yiwa arewa kallon masu la'akari da addini wajen zabe a matsayin daliban tarihi da suka gaza, rahoton Punch.

Ya ce:

"Mutane na buga siyasa da zahiri. A al'adance, arewa ba ta zabe kan addini ko kabilanci."

Kara karanta wannan

2023: Babban Jigon PDP Ya Faɗi Sunayen Jihohin Da Atiku Zai Sha Kaye a Zabe Da Dalilai

Ya kuma bayyana cewa arewa ta zabi M.K.O Abiola a zaben 1993, ba wai saboda addini ba sannan ta zabi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2011 maimakon Atiku ba tare da la'akari da adini ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba bai kowa kunya ba tsawon lokacin da ya dauka yana mulki domin dai a cewarsa ya cika alkawarin da ya daukarwa yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng