Na Yi Alkawarin Zan Yi Wa Yan Najeriya Aiki Iya Karfina, Shugaba Buhari

Na Yi Alkawarin Zan Yi Wa Yan Najeriya Aiki Iya Karfina, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu
  • Shugaban ya ce a lokacin kamfe ya yi alkwarin yi wa Najeriya da mutanen cikinta aiki daidai karfinsa
  • Shugaban APC na ƙasa, Sanata Ahmad Lawan, Femi Gbajabiamila, Tinubu da Shettima na cikin tawagar Buhari

Bauchi - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ya ɗauki alƙawari tun a baya cewa zai bauta wa Najeriya da mutanen da ke cikinta iyakar karfinsa.

Shugaba Buhari ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar gaisuwa ga Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Adamu, a wani ɓangare na Ralin ɗan takarar shugaban kasa na APC a Bauchi.

Shugaban kasa Buhari da Sarkin Bauchi.
Na Yi Alkawarin Zan Yi Wa Yan Najeriya Aiki Iya Karfina, Shugaba Buhari Hoto: Bauchi News
Asali: Facebook

Vanguard ta rahoto Buhari na cewa:

"A 2003 da 2012 na kai ziyara baki ɗaya kananan hukumomi 774 da ke ƙasar nan. A 2019 lokacin da nake neman tazarce na samu ikon zuwa baki ɗaya jihohin Najeriya."

Kara karanta wannan

Gwamna Kuma Farfesa Ya Bayyana Mutum Ɗaya Tilo da Zai Iya Ceto Najeriya a 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka a nan ne na ɗauki alkawari kuma na sha alwashin zan yi wa Najeriya da yan ƙasa aiki bakin karfin da Allah ya bani."

Shugaban ƙasan wanda ya nuna jin daɗinsa da irin tarbar da aka masa a fadar Sarkin, ya gaba wa gwamna Bala Muhammed bisa ayyukan alherin da ya zuba wa al'umma a Bauchi.

Da yake jawabi, Sarkin Bauchi ya miƙa godiyarsa ga shugaban kasa bisa wannan ziyara da ya kai masa kana ya roki 'yan siyasa da su yi siyasa babu gaba.

Yayin da yake yaba wa Ƙauran Bauchi bisa baiwa kowace jam'iyyar siyasa dama a Bauchi, Basaraken ya yi wa shugaban kasa Addu'ar Allah ya sauke shi lafiya.

The Nation ta ruwaito cewa Buhari ya ziyarci fadar Sarkin ne tare da rakiyar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila.

Kara karanta wannan

2023: Wani Gwamnan APC Ya Janye Daga Kamfen Bola Tinubu? Gaskiya Ta Bayyana

Sauran sun haɗa da dan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, abokin takararsa, Kashim Shettima, da sauran jiga-jigan siyasa.

Matsala ta faru a taron APC na Bauchi

A wani labarin kuma An Shiga Rudani Yayin da Gangamin APC Ya Zo Karshe Ba Zato Ba Tsammani

Rahotanni sun bayyana ana tsaka da taron ne sauti ya ɗauke kuma duk kokarin shawo kan lamarin ya ci tura.

Hakan ya tilastawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin barin wajen tare da mukarrabansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel