Zaben 2023: Atiku Ya Rasa Halayen Zama Shugaban Kasa a Najeriya, APC

Zaben 2023: Atiku Ya Rasa Halayen Zama Shugaban Kasa a Najeriya, APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta maida martani kan kiran da PDP ta yi hukumomi su kama Bola Ahmed Tinubu
  • Bayo Onanuga, a wata sanarwa ya ce tun bayan bayyanar gaskiya da murya, Atiku da PDP suka fara shure-shure
  • Kwamitim kamfen Tinubu/Shettima yace yana nan kan bakarsa cewa Atiku bai da halaye na zama shugaban Najeriya

Abuja - All Progressives Congress (APC) tace ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, "Ba shi da hali mai kyau na zama shugaban kasa a Najeriya."

Bayo Onanuga, mai magana da yawun kwamitin kamfen Tinubu/Shettima (PCC-APC) ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

Ya kuma ƙara jaddada kira ga mahukunta da su kama tare da hukunta tsohon mataimakin shugaban ƙasan bisa zargin tafiyar da Special Purpose Vehicles (SPVs) da nufin karkatar da dukiyar gwamnati.

Kara karanta wannan

PDP ta fadawa Buhari ya fatattaki shahararren Ministansa, ta fadi zunubin da ya aikata

Atiku da Tinubu.
Zaben 2023: Atiku Ya Rasa Halayen Zama Shugaban Kasa a Najeriya, APC Hoto: Atiku, Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust tace sanarwan da APC ta fitar martani ne ga kalaman PDP na kira ga hukumar NDLEA da EFCC sun gayyaci Bola Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babbar jam'iyyar hamayya watau PDP ta yi zargin cewa Tinubu na da hannu a badakalar da ta shafi kasuwancin miyagun kwayoyi a shekarar 2015, kamar yadda Punch ta rahoto.

APC ta maida martani

Da yake martani kan haka, kwamitin kamfen APC ya ce:

"Ya bayyana a zahiri cewa har yanzun PDP da Atiku Abubakar ba su farfaɗo ba daga tona asirin da PCC-APC ya masu makon da ya gabata."

A taron manema labarai da suka kira kwanan nan, kwamitin kamfen APC ya ɗiga ayar tambaya kan halin Atiku da har yau yake cikin tseren neman takara bayan saƙon murya da ya fito na almundahanarsa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Bukaci NDLEA Ta Kama Bola Tinubu, Ya Bayyana Dalilai

Sanarwan da Onanuga ya fitar jiya Lahadi ta ce:

"Tun da wannan kwai ya fashe da kuma matakin shari'ar da aka ɗauka don umartar mahukunta sun yi aikinsu, Atiku da PDP suke ta faman kame-kame don sakaya batun."
"Maimakon Atiku ya nemi afuwar yan Najeriya bisa cin amanar da ya yi a Ofis kamar na mataimakin shugaban kasa, sai masu karesa suka ci gaba da haƙo a ramin da suka tsinci kansu."
"Sabon sumfurin wasan barkwancin PDP da Atiku duk borin kunya ne da ƙara tabbatar abinda ake zargi, ba ta yadda zai taɓa Tinubu. Muna nan kan bakarmu, Atiku ba shi hali mai kyau na zama shugaban kasa."

Tinubu Ne Kadai Zai Iya Gayara Najeriya, Gwamna Ben Ayade

A wani labarin kuma Gwamnan jihar Kuros Riba ya bayyana hasashensa game da wanda zai iya gyara Najeriya bayan shugaba Buhari

Farfesa Ben Ayade, gwamnan jihar Kuros Riba na APC, yace Bola Tinubu zai iya ɗaga darajar Najeriya zuwa gaba idan ya gaji Buhari.

Kara karanta wannan

Ba Wanda Zai Ci Bulus: Atiku Ya Gindaya Sharadin Baiwa Mambobi da Manyan PDP Mukami Idan Ya Ci Zabe

Farfesa Ayade yace Tinubu zai ɗauki ayyukan raya ƙasa da ci gaban jihar Kuros Riba da matukar muhimmanci idan aka zaɓe shi ya zama shugaban ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262