Jam’iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Mambobin Jam’iyyar Su Kwankwaso a Kano

Jam’iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Mambobin Jam’iyyar Su Kwankwaso a Kano

  • Jam’iyyar APC a ranar Lahadi ta tarbi karin masu sauya sheka a jihar Kano gabannin babban zaben 2023
  • Mambobin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta su Kwankwaso sun koma jam'iyya mai mulki a kananan hukumomin Minjibir da Ungogo
  • Gwamna Abdullahi Ganduje ya cika da murna yayin da yake yi wa masu sauya shekar maraba da zuwa cikinsu

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya cika da farin ciki yayin da ya tarbi mambobin jam'iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP wadanda suka sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC) gabannin zaben 2023.

Mambobin jam'iyyar NNPP ta su Kwankwaso sun yi watsi da jam'iyyarsu sannan suka koma APC a kananan hukumomin Munjibir da Ungogo da ke jihar Kano, a ranar Lahadi, 22 ga watan Janairu.

Kwankwaso da Ganduje
Jam’iyyar APC Ta Yi Babban Kamu Na Mambobin Jam’iyyar Su Kwankwaso a Kano Hoto: Rabiu Kwankwaso, Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ganduje ya hadu da dandazon magoya baya wadanda suka cire jajjayen hulunarsu na Kwankwasiyya sannan suka jefar da su a filin kamfen, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Damammakin da manyan yan takarar shugaban kasa 4 ke da shi a jihohi 5 mafi yawan kuri'u

Sun yi ikirarin cewa APC ce jam'iyya daya tilo da ta cika muradansu da mafarkansu na jihar Kano da Najeriya mai inganci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganduje ya yi wa tsoffin mambobin Kwankwasiyya maraba da zuwa APC

Ganduje, wanda shine kusa shugaban APC a jihar, ya yi wa masu sauya shekar karkashin jagorancin shugaban Kwankwasiyya a Minjibir, Ibrahim Hamza, maraba da zuwa sannan ya taya su murnar wannan shawara da suka dauka.

Ya kuma yaba da yadda dandazon jama'a suka hallara a wajen gangamin kamfen din yana mai cewa ba a taba irinsa ba, rahoton Daily Post.

Sakamakon haka, gwamnan ya bukaci mutane da su zabi dukkanin yan takarar APC a babban zabe mai zuwa.

Ya kuma gabatar da tutar APC ga yan takarar majalisar wakilai da majalisar dokoki na jiha.

Dama Minjibir da Ungogo ta APC ce, Abdullahi Abbas

Kara karanta wannan

NNPP Ta Ruɓe, An Bayyana Wanda Ya Kamata Kwankwaso Ya Janye Wa Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Da farko, Abdullahi Abbas, shugaban APC a jihar, ya bayyana cewa APC ce ke lashe zabe a Minjibir da Ungogo sannan cewa za ta ci gaba da hakan a zabuka masu zuwa.

Abbas ya yaba da yadda magoya bayan APC suka halarci gangamin sannan ya bukaci mutanen yankin da su ci gaba da zaben APC don ci gabansu.

A wani labarin kuma, mun ji cewa jam'iyyun siyasa da yan takarar shugaban kasa na ta kokarin shirya dabaru don ganin sun kawo jihohi mafi yawan masu rijistan zabe a 2023.

Lagas, Kano, Kaduna, Katsina da Ribas sune jihohi biyar mafi yawan masu rijista a zaben 2023 kamar yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta sanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel