Mamban Kwamitin Amintattun APC Ya Janye Daga Bayan Tinubu, Ya Koma Obi

Mamban Kwamitin Amintattun APC Ya Janye Daga Bayan Tinubu, Ya Koma Obi

  • Mamban kwamitin amintattu na APC ya jingine Bola Tinubu, ya bayyana wanda zai goyi baya a 2023
  • Prince Apugo, jigon siyasa mai faɗa a ji a jihar Abiya ya ce Peter Obi na da gogewa da kwarewar zama shugaban kasa
  • Jigon siyasan ya bayyana cewa yana tare da ɗan takarar gwamnan LP a jihar Abiya a zabe mai zuwa

Abia - Wani babban ƙusa a siyasar jihar Abiya kuma mamban kwamitin amintattu (BoT) a jam'iyyar APC, Prince Benjamin Apugo, ya ayyana goyon bayansa da Peter Obi.

Jaridar Vanguard ta rahoto jigon siyasar na cewa gogewa, gaskiya da tarihin nasarorin dan takarar shugaban kasa na LP, ya sa ya yi wa sauran 'yan takarar fintinkau.

Tinubu da Peter Obi.
Mamban Kwamitin Amintattun APC Ya Janye Daga Bayan Tinubu, Ya Koma Obi Hoto: Bola Tinubu
Asali: UGC

Jigon jam'iyyar APC ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a mahaifarsa Ibeku Umuahia, jihar Abiya ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Motar Ɗan Takarar Gwamna Wuta

Mista Apugo ya kuma tabbatar da cikakken goyon baya da ɗan takarar gwamna a inuwar Labour Party, Dr Alex Otti, inda a cewarsa yana da kwarewar da ake nema don sake gina sabuwar Abiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bana tare da dan takarar APC a Abiya - Prince Apugo

Prince Apugo ya musanta rahoton dake yawo cewa ya ayyana goyon baya ga ɗan takarar gwamnan APC a jihar Abiya, High Chief Ikechi Emenike. Yace rahoton ba shi da tushe.

Yace bai taɓa sanya albarka a burin Emenike na zama gwamna ba kuma ya yi gargaɗi da kakkausan murya kan duk wani yunkurin amfani da shi don samun nasara.

Apugo ya zargi gwamnatin tarayya ta APC da nuna halin ko in kula da jihar Abiya, ya yi ikiratin cewa babu wani muhimmmin aikin tarayya a jihar dake kudu maso gabas.

"Jam'iyyar APC ba abinda ta yi wa Umuahia da jihar Abiya baki ɗaya, yankin da aka haife ni," ya faɗa cikin nadama.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar M/Gwamna Ya Juyawa Jam’iyyarsa Baya, Za a ba Shi Kujera a Mulkin APC

Yace APC ba ta yi wa Ibo komai ba don haka ya yi kira ga masu katin zabe su natsu su tantance shugabannin da zasu zaɓa a watan Fabrairu da Maris.

Jam'iyyar PDP Ta Nemi NDLEA, EFCC Su Damke Bola Tinubu Na APC

A wani labarin kuma Kwamitin kamfen Atiku Abubakar ya yi kira ga mahukunta su cafke ɗan takarar APC, Bola Tinubu

Bwala, mai magana da yawun PCC-PDP yace ɗan takarar shugaban kasan yana da tambayoyin da ya kamata ya amsa gane wata badakala tsakaninsa da ƙasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel