An Samu Rashin Jituwa a Jam’iyyar LP, Jagorori Za Suyi Fito na Fito da Peter Obi
- Shugabannin jam’iyyar LP na reshen Kano su na kuka da yadda ake gudanar da yakin neman zabe
- Jagororin yakin neman zabe na zargin Datti Baba-Ahmed da cusa ‘yanuwa da abokan arziki a kamfe
- Irinsu Mohammed Zarewa, Bashir I. Bashir, Balarabe Wakili da Idris Dambazau su na ganin da sake
Kano - Idan abubuwa ba su canza a reshen jihar Kano ba, jagororin jam’iyyar LP za su kauracewa Peter Obi yayin da yake shirin zuwa yawon kamfe.
Daily Nigerian ta rahoto cewa shugaban kwamitin yakin zaben LP a Kano, Mohammed Zarewa da Bashir I. Bashir ba su ji dadin yadda ake tafiya.
Shugaban kwamitin da ‘dan takararar Gwamnan Kano da irinsu Balarabe Wakili da Idris Dambazau su na kukan jam’iyyar LP ba ta tafiyar zabe da su.
Peter Obi zai shirya gangami a filin wasa na Sabon Gari da ke garin Kano a ranar Lahadi, sannan shi da magoya bayansa a zaben 2023 za su yi tattaki.
Datti Baba-Ahmed ya kawo cikas?
Rahoton da aka fitar ya nuna jagororin kwamitin yakin neman zaben da ‘dan takaran Gwamnan Kano a karkashin LP su na kuka da Datti Baba-Ahmed.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Ya ‘yan jam’iyyar su na korafin cewa Datti Baba-Ahmed ya maida sha’anin kamfe na ‘yan gidansu da danginsu, ba a yin zama da wadanda suka dace.
Wata majiya ta shaida cewa ‘dan takaran mataimakin shugaban kasar ya dauko Surukinsa, Yusuf Bello-Maitama a matsayin shugaban kamfe na Arewa.
Bayan haka, ‘dan takaran ya zabi kawunsa, Audi Mohammed a matsayin Darekta Janar na yakin neman zaben jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso yamma.
Daga cikin zargin shi ne babban jami’in da ke kula da kudi a jami’ar Baze shi ne wanda aka dauko ya jagoranci bangaren kudi a kwamitin yakin zaben LP.
Anthony Okafor da Uche Okafor
Majiyar ta ce har nada Anthony Okafor da aka yi ya jagoranci kamfen LP a Kano kuskure ne.
Inda ake gani jam’iyyar adawar ta tafka wani kuskure shi ne zabo Uche Okafor domin ya tattaro magoya baya a Kano, a maimakon a nemi Bahaushen jihar.
Shugaban LP a Kano, Mohammed Raji ya ce shi ba zai kauracewa yakin neman zaben ba, amma yana goyon bayan matakin da ‘yan jam’iyyar suka dauka.
Kira ga Kwankwaso
An samu labari cewa ungiyar Kungiyar Northern Liberal Democratic Movement ta ce zai fi kyau a ‘dan takaran Jam’iyyar NNPP ya bi bayan Atiku Abubakar.
Babban Sakataren NLDM ya ce da wahala jam’iyya mai kayan marmari ta iya kai labari, don haka take so Rabiu Kwankwaso ya hakura da takararsa.
Asali: Legit.ng