Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a Ribas

Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a Ribas

  • Gwamna Ribas, Nyesom Wike, ya gargaɗi kwamitin yakin neman zaben Atiku su shiga taitayinsu
  • Wike, jagoran G-5 gargadi daraktan kamfen na Ribas kar ya sake zuwa filin Adokiye Amiesimaka sai lokaci ya yi
  • Ya yi barazanar cewa zai fasa baiwa kwamitin kamfen Atiku damar amfani da filin idan suka ci gaba da zuwa tun yanzu

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi barazanar soke damar da ya baiwa kwamitin kamfen shugaban ƙasa na amfani da filin wasan Adokiye Amiesimaka yayin Ralin Atiku Abubakar.

Gwamna Wike yace Daraktan kwamitim kamfen Atiku (PCC) a jihar Ribas, Dakta Abiye Sekibo, ya fara amfani da wurin watanni gabanin ranar da aka sahale masu 11 ga watan Fabrairu.

Gwamna Wike da Atiku.
Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Soke Wurin da Atiku Zai Yi Kamfe a Ribas Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wike yace ba da wurin, wanda PCC ta samu kyauta, ba zai yuwu su fara zagaye suna zuwa ciki ba har sai awanni 48 gabanin ainihin ranar da aka amince musu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Ganduje Ta Jawo Farfesa Jega, Ta Hada Shi da Wani Babban Nauyi a Najeriya

Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan ya yi wannan barazana ne a wurin kaddamar da kamfen PDP na ƙaramar hukumar Oyingbo ta jihar Ribas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace Sekibo bai da ikon zuwa ya fara nuna iko da filin wasan wata ɗaya gabanin ranar da aka amince su gudanar da taron.

Gwamna Wike ya gargaɗi Sekibo ya shiga taitayinsa kar ya harzuka gwamnatin Ribas ta hanyar nuna iko da filin wasan da ya ke mallakin jiha, idan kuma ba haka zai soke damar.

The Cable ta rahoto a kalamansa Wike na cewa:

"Ina amfani da wannan damar na gargaɗi Sekibo, mun yarda ɗan takararku na shugaban ƙasa ya yi amfani da filin wasan Adokiye Amiesimaka ranar 11 ga watan Fabrairu, baka da ikon zuwa filin tun yanzu."
"Ba zamu baku dama ku fara amfani da wurin ba yanzu, sai kwana biyu kafin ranar da kuka shirya taro, ba wanda ya baku wata ɗaya."

Kara karanta wannan

Babban Sarki Mai Martaba Ya Tsoma Baki a PDP, Ya Gaya Wa Atiku Abinda Ya Dace Ya Yi Wa Gwamnonin G-5

"Saboda haka idan ka sake zuwa ka tilasta shiga filin zan soke damarku ta amfani da wurin, in ka isa ka sake zuwa ni kuma zan soke, ba abinda zai faru, idan sama zata faɗo zamu so haka."

Olubadan Ga Atiku: Ka Sasanta da Makinde da Sauran Gwamnonin G5

A wani labarin kuma Olubadan na ƙasar Ibadan ya roki Atiku ya gaggauta sasanta wa da gwamnonin G-5 gabanin ranar zabe

Babban Basarken, wanda ya bayyana Atiku a matsayin abokinsa, ya ce ba ya jin dadin rigingimun da ke faruwa a cikin jam'iyyar PDP.

Tun bayan zaben fidda ɗan takarar shugaban kasa na PDP, jam'iyyar ba ta sake samun kwanciyaɗ hankali a cikin giɗa ba har yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel