Olubadan Ga Atiku: Ka Sasanta da Makinde da Sauran Gwamnonin G5

Olubadan Ga Atiku: Ka Sasanta da Makinde da Sauran Gwamnonin G5

  • Olubadan na kasar Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya roki Atiku Abubakar ya sasanta da gwamnonin G-5
  • Sarkin ya nemi Atiku ya sake duba matsayin Sarakuna a kasar nan idan ya samu nasara a babban zabe mai zuwa
  • Atiku ya kaiwa Basaraken ziyarar girma yau Alhamis gabanin Ralin yakin neman zabensa a Oyo

Oyo - Sarki mai daraja na ƙasar Ibadan, wanda ake kira Olubadan, Oba Lekan Balogun, ya roki dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya sulhunta da gwamna Makinde da sauran gwamnonin G-5.

Babban Basarken, wanda ya bayyana Atiku a matsayin abokinsa, ya ce ba ya jin dadin rigingimun da ke faruwa a cikin jam'iyyar PDP, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Atiku ya ziyarci Olubadan.
Olubadan Ga Atiku: Ka Sasanta da Makinde da Sauran Gwamnonin G5 Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Olubadan ya ce ya kamata Atiku ya hanzarta yin duk mai yuwuwa wurin haɗa kan jam'iyyar gabanin babban zaben shugaban kasa 2023.

Kara karanta wannan

Ko Sama Ko Kasa Ba a Ga Gwamnan Oyo Ba a Wajen Yakin Neman Zaben Atiku Da ke Gudana a Ibadan

Gwamnonin G-5 sun ƙunshi Nyesome Wike (Ribas); Samuel Otorm (Benuwai); Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Okezie Ikpeazu (Abiya) da Seyi Makinde(Oyo).

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake jawabi yayin da ya karɓi bakuncin Atiku ranar Alhamis a fadarsa dake Ibadan, Olubadan yace Atiku na bukatar wannan sulhu domin samun nasara a babban zabe.

Bugu da kari, Sarkin ya roki Atiku idan ya zama shugaban kasa kar ya manta da Sarakunan gargajiya, warware matsalar tsaro kuma ya amince Ibadan ta zama jiha mai zaman kanta.

Zan dawo da martabar Sarakuna - Atiku

Da yake jawabi a fadar Sarkin, Atiku ya bayyana cewa gwamnatin PDP zata dawo da martabar Sarakunan gargajiya kuma zata tabbatar da alaƙa tsakanin Sarakuna ta kara karfi, Vanguard ta ruwaito.

"Ina tuna matsayin Sarakuna a lokacin mulkin mallaka, su ke da alhakin tabbatar da doka da oda a yankunan Masarauntarsu, gwamnatin PDP zata duba Masarautu domin dawo da aminci da haɗin kan Najeriya."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Atiku Abubakar Ya Dira Jihar Matashin Gwamnan G-5, Ya Shiga Matsala Tun a Filin Jirgi

"Zamu aiwatar da sauya fasalin kasar nan, mu zauna da mutanen mazabu daban-daban saboda mu basu yancin cin gashin kai da kasafi domin ta haka ne za'a dama da kowa a cigban tattalin arziki."

- Atiku Abubakar.

A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya gargadi shugabannin PDP kan rikon sakainar kashin da suke wa batun sulhu da G-5

Ortom, daya daga cikin jagororin tawagar gaskiya, yace kar a zargi kowa a zargi PDP idan har G-5 ta rufe kofar neman maslha da tsagin su Atiku.

Bayan haka gwamnan ya bayyana dan takarar da ya kwanta masa a rai duba da yanayin da Najeriya ta tsinci kanta a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel