Saura Kiris Na Zabi Wanda Zan Marawa Baya a Zaben Shugaban Kasa, Wike

Saura Kiris Na Zabi Wanda Zan Marawa Baya a Zaben Shugaban Kasa, Wike

  • Gwamna Wike ya yi karin haske kan lokacin da zai bayyana wanda tawagarsa zasu marawa baya a zaben watan Fabrairu
  • Wike, jagoran gwamnonin G-5 ya raba gari da tsagin Atiku ne saboda kafa sharadin shugaban PDP ya yi murabus
  • A wurin taron ralin kamfe yau Talata a Ribas, gwamnan ya ce suna gab da yanke wanda zasu goyi baya a zaben shugaban kasa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyeson Wike, ya ce ya kusa karkare tattaunawar da yake da abokanansa game da ɗan takarar shugaban kasan da zasu marawa baya a zaben 25 ga watan Fabrairu.

Wike ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da kamfen PDP na ƙaramar hukumar Ikwerre jihar Ribas wanda ya gudana a Cocin St. Martin’s Anglican, Omagwa ranar Talata.

Gwamna Wike na jihar Ribas.
Saura Kiris Na Zabi Wanda Zan Marawa Baya a Zaben Shugaban Kasa, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Gwamnan yace abun sha'awa da babban zabe mai zuwa shi ne babu kofar da jami'an tsaro zasu yi magudi ko su ba mutane tsoro a sauya sakamakon zaben, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

A kalaman Wike ga dandazon magoya bayan da suka halarci Ralin ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wannan lokacin, ba sojan da zai tsorata ku, babu wani jami'i ko dan sanda da zai iya wani abu yanzu kowa na da yanci kan kuri'arsa. Ba wanda zai tsorata ku ko ya zo muku da wani labari."
"Muna son ganin dukkan kuri'unku a Akwatu ɗaya tun daga zaben gwamna da na mambobin majalisar dokoki. Ɗayan kuma (zaben shugaban kasa) muna gab da karkarewa, za'a fada muku da zaran mun gama."
"Mu cikakun 'yan kasa ne, ba wanda ya isa ya zo nan ya mana babatu, na kalulanci hakan, kowa na da ikon buga wasan barkwancinsa, zamu yi magana da babbar murya cewa mu ƴan Ribas ne."

Yaushe Wike zai bayyana dan takarar da yake so?

Gwamnan Wike ya bukaci mazauna jihar Ribas su kwantar da hankalinsu nan gaba kadan zai bayyana inda zasu jefa kuri'unsu a zaben shugaban kasa, the nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Wike ya ci gaba da cewa:

"Idan muka tashi daga nan kowa ya koma gida ya fara shiri kafin lokaci ya yi. Da kun ji mun kada kararrawa, ku sani mun yanke hukunci na karshe."

A wani labarin kuma Yayin ranar zabe ta matso, Bola Tinubu Ya Gamu da Babbar Matsala a Jihar Shugaba Buhari

Ana gab da zaben shugaban kasa, APC ta kara ramewa a jihar Katsina, jihar da Buhari ya hito a arewa maso yammacin Najeriya.

Jirgin yakin neman zaben Yakubu Lado ya raba APC da dubbannin mambobi zuwa PDP a yankin karamar hukumar Ingawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel