Gwamnati ta Haramtawa Atiku Wajen Yin Kamfe, Ta Kawo Dalilin Hana Shi Filin Wasa
- Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ogun ta rubuta takarda, tana neman izinin yin amfani da filin wasan MKO Abiola
- Gwamnatin Ogun ta ki yarda ayi amfani da filin wasan, ta kuma kawo hujjar kin amincewa da rokon Jam’iyyar
- Wani jami’in ma’aikatar harkokin matasa da wasanni na jihar Ogun ya ce ana gyaren filin a daidai lokacin nan
Ogun - Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnatin jihar Ogun ta bata damar yin amfani da babban filin wasan MKO Abiola domin shirya taron kamfe.
Punch ta ce ma’aikatar kula da harkar matasa da wasanni na jihar Ogun ba ta amince da wannan roko da jam’iyyar adawar ta kawo gabanta ba.
PDP ta aika da wasika zuwa ga Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kudu maso yammacin kasar domin shirya gangamin Atiku Abubakar.
A takardar, sakataren jam’iyya na reshen Ogun, Sunday Solarin ya yi bayanin yadda gwamnati ta hana su yin amfani da wannan filin wasan a baya.
Ba yau aka fara ba - Sakataren PDP
Solarin ya ce a watan Afrilu sun roki gwamnati ta ba su filin wasan MKO Abiola domin shirya zaben tsaida ‘yan takara, amma aka yi banza da su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jam’iyyar PDP ta fara shirun da gwamnatin Dapo Abiodun tayi masu a matsayin rashin amincewa, don haka wannan karo suka sake neman sabon izini.
Kamar yadda ICIR Nigeria ta kawo rahoto, ma’aikatar wasanni da harkokin matasa ta amsawa jam’iyyar da cewa ba za a iya ba su filin wasan a yanzu ba.
Amsar ta fito daga ofishin Darektan gudanarwa na ma’aikatar a madadin sakataren din-din-din.
Ana gyaran filin yanzu haka - Gwamnati
I.A Kuforiji ya ce a halin yanzu gwamnati tana wasu manyan gyare-gyare a filin wasan, saboda haka ba za a iya amfani da shi domin taron siyasa ba.
Kamar yadda I.A Kuforiji ya shaidawa PDP, gyaran da ake yi ya shafi bangaren masu kallon wasa da kuma wasu muhimman wurare a harabar babban filin.
A lokacin da ake wannan magana, labarai na yawo cewa a filin wasan aka buga kwallon kafa tsakanin wasu kungiyoyi biyu a gasar cin kofi na Iseya.
Babu jituwa tsakanin Atiku da su Fayose?
A jiya ne aka samu labari, dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya je kamfe a Ekiti, amma ‘yan takara da shugabannin jam’iyya sun yi watsi da shi.
Duk da haka, taron Jam’iyyar adawar ya cika sosai, wannan ya jawo saura kiris Atiku ya zubar da hawaye saboda farin cikin irin kaunar da aka nuna masa.
Asali: Legit.ng