Bidiyon Obasanjo Sanye da Kayan Makarantar Sakandare, Yana Tattaki da Tsofaffin Dalibai

Bidiyon Obasanjo Sanye da Kayan Makarantar Sakandare, Yana Tattaki da Tsofaffin Dalibai

  • Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegub Obasanjo, babu shakka cike ya ke da kar sashin da nishadi a rayuwarsa
  • Obadanjo ya fallasa hakan a sabon bidiyo da ya bayyana sanye da kayan makarantar Baptist Boys High School Ogun
  • Tsohon sojan ya hadu da wadanda ya wuce a makaranta tare da tattakawa suka jera duk a cikin murnar cikar makarantar shekaru 100 da kafuwa

Ogun - Cif Olusegun Obasanjo ya nuna yadda yake cike da karsashi da karfin jiki yayin da ya ke dalibin makarantar sakandare.

Obasanjo
Bidiyon Obasanjo Sanye da Kayan Makarantar Sakandare, Yana Tattaki da Tsofaffin Dalibai. Hoto daga Ope Banwo II
Asali: Facebook

Tsohon shugaban kasan Najeriya an gan shi a wani bidiyo da aka wallafa a Facebook ranar Litinin, 16 ga Watan Janairu inda ya ke sanye da kayan motsa jiki na Baptist Boys High School, tsohuwar makarantar da ya halarta.

A bidiyon da wani Ope Banwo II ya wallafa, Obasanjo ya bayyana cike da Ko shine lafiya cikin tsofaffin dalibai sa’o’insa yayin da suke tattaki a gari.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Kama Jarumin da ya Caka wa Makwabcinsa Wuka a Kirji kan N1,000

“Baba OBJ yana taka rawar babban firifet yayin da BbHS ta cika shekaru 100 da kafuwa a tattakin da suka yi. Kada ku yi ganganci da Kaka OBJ. Har yanzu akwai abun a jiki. Yadda dai firifet ke tsinka mari a wancan lokacin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wannan ya tuna min lokacin da na ke makarantar kwana ta Ijebu Ode Grammar. Na gaba da ni ba su yi wasa da ni ba. Sir Pawpaw, Sor Adelana, Sir Japhet, Sir Shina ballantana Sir Oyen duk ‘yan ajin 1977, 78 da 79. Allah kadai ya san yawan ku don ku mududduke ni.”

Kalla bidiyon:

Abubuwan mamakin Obasanjo

Ba wannan bane na farko a rayuwar tsohon shugaban kasan da ya nuna karsashinsa da kwarin jikinsa.

Ba sau daya ko biyu ba, ya saba gwada kwarewarsa a rawa inda ya ke kwasar rawa cike da kwarewa da Gwanintarsa a wuraren bukukuwa.

Kara karanta wannan

Sharri aka min: Dan sandan da bindige lauya mai juna biyu ya musanta zargin kisa

Tsohon shugaban kasan na mulkin Soja da farar hular har keke Napep ya taba dauka ya zagaya gari duk don nuna cewa ba duka matukan adaidaita sahu bane mutanen banza.

Bidiyon mai cike da abun mamaki ya bazu inda aka gano cewa ya zagaya ne a a cikin birnin Abeoukuta na jihar Ogun inda gidansa ya ke kuma ya ke zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel