Kashim Shettima Yana Ganawar Sirri Da Rochas Okorocha A Abuja

Kashim Shettima Yana Ganawar Sirri Da Rochas Okorocha A Abuja

  • Sanata Kashim Shettima, dan takarar mataimakin shugaban kasa na All Progressives Congress, APC, ya ziyarci Sanata Rochas Okorocha
  • Rahotanni sun nuna cewa Sanata Shettima ya isa gidan Okorocha da ke birnin tarayya Abuja a daren ranar Asabar
  • Kawo yanzu ba a tantance ainihin dalilin yin taron ba domin sun saka labule amma ana zaton tana da alaka da zaben shugaban kasa

FCT Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Sanata Kashim Shettima, a halin yanzu yana ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Imo a gidansa da ke Maitama Abuja.

An ce Shettima ya isa gidan sanatan mai wakitan Imo ta Yamma ne misalin karfe 10:15 na dare kuma suka shiga taron kai tsaye bayan gaisuwa, rahoton The Punch.

Kashim Da Okorocha
Kashim Shettima Yana Ganawar Sirri Da Rochas Okorocha A Abuja. Hoto: Nairaland
Asali: Facebook

Ana can ana cigaba da taron har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan Bindiga sun budewa gidan dan takarar majalisar wakilai wuta, sun kashe yayansa

Ba a san dalilin taron nasu ba a yanzu amma ana kyautata zaton ba zai rasa alaka ba da zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata kungiyar matasa na jam'iyyar APC ta ce ba za ta yi Shettima ba a zaben 2023

A yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023, jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta gamu da wani cikas daga matasa daga kudu maso gabas.

Matasan da suka fito daga yankin da dan takarar mataimakin shugaban kasar, Sanata Shettima ya fito sun yi barazanar cewa ba za su zabe shi ba.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ta samu wani sakon manema labarai, mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar matasan, Shu'aibu Tilde, in ta ce Shettima ya yi watsi da su tunda ya ga an ce shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC.

Kara karanta wannan

2023: Hantar PDP, Atiku Ta Kada Yayin Da Yar Tinubu Ta Ziyarci Babban Dattijon Arewa, Bayanai, Hotuna Sun Fito

Sanarwar ta ce:

"Wannan shine dalilin da yasa da dama cikin yan jam'iyyar mu suka ficewa, ciki har da shugaban matar mu, Hajiya Amina Mangal, wacce ta sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP."

Shettima ya yi magana kan tattaunawarsu da Kwankwaso ya marawa Tinubu baya a zaben 2023

A bangare guda, Sanata Kashim ya yi magana dangane da yiwuwar hadin kai tsakanin jam'iyyar APC, da Rabiu Kwankwaso na jam'iyyar NNPP gabanin zaben 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Borno ya ce shi da kansa zai nemi Sanata Kwankwaso a daidai gabar da ta dace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel