Matasan Jam'iyyar APC A Arewa Maso Gabas Na Shirin Bawa Shettima Ruwa

Matasan Jam'iyyar APC A Arewa Maso Gabas Na Shirin Bawa Shettima Ruwa

  • Yanzu dai neman magoyan baya ake, bama iya magoya baya ba harda yan dangwale wajen zasu jefa kuri'a a akwati
  • kashim Shettima dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, na fuskantar barazana daga 'ya 'yan jami'iyyarsa daga yankin arewa maso gabas
  • Wasu gugun matasa ne ke shirin ballewa daga jam'iyyar APC a jihohin Barno, Yobe, Gombe da sauransu muddin ba'a biya musu bukatunsu ba

Abuja - Kasa da wata daya ya rage a jefa kuri'ar babban zaben Nigeria, amma jam'iyyar APC a yankin arewa maso gabas na neman fadawa rikicin wasu matasa.

Matasan sunyi barazanar kin marawa dan takarar mataimakain shugaban kasa, Kashim Shettim a zabe mai zuwa.

Matasan jam'iyyar APC din karkashin jagorancin masu ruwa da tsakinsu, sunyi tutsu game da mubaya'ar da sukai wa tsohon gwamnan jihar na Barno da kuma yin barazanar yakarsa a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP

Kashim
Matasan Jam'iyyar APC A Arewa Maso Gabas Na Shirin Bawa Shettima Ruwa Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa da suka rabawa manema labarai jiya a Abuja wanda jaridar Leadership ta samu, shugaban matasan jam'iyyar APC na yankin arewa maso gabas Shu'aibu Tilde, yace Shettima ya watsar dasu lokacin da yaga an ce shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar

"Dalilin haka yasa da yawa daga cikin yayan wannan jam'iyyar suka fice, ciki harda shugabar matar mu, Hajiya Amina Mangal wadda ta koma jam'iyyar PDP. "

Haka Yusuf Banki ma shi da wasu magoya baya kusan su 500,000 da suka fice daga cikin jam'iyyar.

sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Muna jin bakin cikin irin wadannan abubuwan da suke faruwa sabida san zuciyar wasu, amma duk da haka mu muna son jam'iyyar mu, dan haka muke kokari dan ganin an ceto ta daga hannun yan sari"

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Atiku da Peter Obi Sun Shiga Matsala, Sun Yi Gagarumin Rashi Ana Gab Da Zabe

Martanin Shettima

Jaridar Vangaurd ta rawaito cewa mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Tinubu/Kashim ya magantu kan wannan batun

Festus Keyamo (SAN), yace irin wannan matsaltsalun na faruwa musamman ma idan zabe ya karato sabida kowa nada bukatar da yake so aa biya masa, amma duk da haka zamu bi wannan batun kuma za'ai ssulhu akai.

Sannan Festus din ya soki lamarin labarin wai ana yawan ficewa daga jam'yyar inda yace kawai ana fada ne dan batawa jam'iyyar suna

Asali: Legit.ng

Online view pixel