Gwamnan Osun Ya Fadi Abin da Za a Rika Tuna Buhari da Shi Bayan Mayun 2023

Gwamnan Osun Ya Fadi Abin da Za a Rika Tuna Buhari da Shi Bayan Mayun 2023

  • Ademola Adeleke ya samu damar ganawa da Shugaban Najeriya a haduwarsu ta farko a Aso Rock
  • Sabon Gwamnan na jihar Osun ya ce tun ba yau ba yake hankoron zama da Muhammadu Buhari
  • Adeleke ya yabi shugaban kasar da cewa gwamnatinsa ta gyara harkar zabe har Duniya tana yabawa

Abuja - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun, ya kai ziyara zuwa ga Mai girma Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 13 ga watan Junairu 2022.

Premium Times ta rahoto Gwamna Ademola Adeleke yana cewa ya kawowa shugaban kasar ziyarar godiya ne domin a dalilinsa ya lashe zabe.

Adeleke yake cewa sabuwar dokar zabe ta shekarar 2022 da aka kawo, ta taimaka sosai wajen zamansa Gwamnan Osun a karkashin jam’iyyar adawa.

Dokar zabe tayi aiki - Adeleke

A watan Fubrairun 2022 ne shugaban kasa ya sa hannu a dokar zabe, zuwa Nuwamban shekarar aka rantsar da Adeleke a matsayin Gwamna

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Najeriya Obasanjo Ya Bada Wasu Shawarwari Masu Dauke Da Hikima Ga Shugaban Najeriya Na Gaba

Da yake jawabi dazu Abuja, Adeleke ya fadawa manema labarai, ganin an yi adalci a zaben da ya lashe, shiyasa ya zo yi wa shugaban Najeriyan godiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aso Rock
Ademola Adeleke da Shugaban Kasa Hoto: www.vanguardngr.com
Asali: UGC
“Ina mai farin cikin fada maku yanzu na ga shugaban kasar mu ya yi kyawun gani, kuma ina mai farin ciki da wannan.
Tun bayan zabe na, nake jin ya dace in zo in ga Mai girma shugaban kasa, in yi masa godiya da ya sa hannu a dokar zabe.
Na amfana da dokar zaben da ya taimaka wajen yin zaben adalci da gaskiya, har kasashen Duniya su na yabawa Najeriya.

- Gwamna Ademola Adeleke

Gwamnan yake cewa ziyarar da ya kai zuwa Aso Rock ta ba shi damar zantawa da Farfesa Ibrahim Gambari a kan taimakon da za a iya yi wa jihar Osun.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Kafa Sharadi 1 Da Zai Sa Ya Yi Wa Inyamurai Aiki Idan Zama Shugaban Kasa a 2023

Femi Adesina a jawabin da ya fitar, ya ce sabon Gwamnan ya dade yana sa ran ganin Buhari, yake cewa inganta harkar zabe zai sa a rika tunawa da shi.

Muhammadu Buhari ya yi alkawarin zai duba bukatun da Gwamna Adeleke ya gabatar masa, Leadership ta fitar da wannan labari a yammacin nan.

Bukatun Adeleke sun hada da gina abubuwan more rayuwa, birane, neman bashi da sauransu.

Ba na cikin wata Jam’iyyar siyasa – OBJ

A wata hira da aka yi da shi, an ji labari cewa Olusegun Obasanjo ya ce ba zai rika bin Peter Obi da jam’iyyar LP zuwa yawon kamfen shugabancin kasa ba.

Cif Obasanjo wanda ya yi mulki a lokacin soja da kuma farar hula, yayi karin haske a kan zargin bankara tsarin mulki domin ya zarce bayan Mayun 2007.

Asali: Legit.ng

Online view pixel