Tinubu Bashi da Wata Cuta Duba da Yadda ya Kwashi Rawar 'Buga', 'Dan Majalisa

Tinubu Bashi da Wata Cuta Duba da Yadda ya Kwashi Rawar 'Buga', 'Dan Majalisa

  • 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Takai/Sumaila a tarayya, Shamsudeen Dambazau, yace Tinubu lafiya kalau ya ke fiye da Kashim Shettima
  • Dambazau ya sanar da cewa, duba da yadda Tinubu ya kwashi rawa tare da girgijewa bayan saka fitacciyar wakar 'Buga' alama ce ta tsananin lafiyarsa
  • Yayi kira ga 'yan Najeriya da su zabi tsohon gwamnan jihar Legas din don shi ne zai iya shawo kan matsalolin Najeriya baki daya

FCT, Abuja - Shamsudeen Dambazau, mamban majalisar wakilai, yace Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na APC yana da lafiya garau.

Bola Tinubu
Tinubu Bashi da Wata Cuta Duba da Yadda ya Kwashi Rawar 'Buga', 'Dan Majalisa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Dambazau 'dan majalisa ne a APC mai wakiltar mazabar Takai da Sumaila a Tarayya, ya sanar da hakan ranar Alhamis a Abuja, jaridar TheCable ta rahoto.

'Dan majalisar wanda 'da ne ga Abdulrahman Dambazau, tsohon ministan harkokin cikin gida, yace Tinubu a baya-bayan nan yayi rawar Buga domin ya nuna lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

'Buga' waka ce wacce Kizz Daniel da Tekno suka rera ta kuma tayi tashe da shuhura a cikin kwanakin nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dambazau yace Tinubu yana da koshin lafiya ba kamar abokin gaminsa ba wanda yace ba shi da cikakkiyar lafiya.

"Tinubu yana da lafiya. Babu wani abu da ke damunsa."

- Yace.

"Idan za ku tuna, a daren jiya Kashim Shettima ya bayyana cewa ya na fama da ciwon sikari kuma ya na da hawan jini.
“Amma Tinubu ba shi da kowanne ciwo. Garau ya ke. Ba ku ga yadda ya kwashi rawar Buga ba? Yana da lafiya. Babu abinda ke damunsa."

Yace Tinubu zai shawo kan matsalolin da ke addabar kasar nan tare da tabbatarwa Najeriya ta dawo tana aiki fiye da baya.

"Dukkan matsaolin da ke addabar Najeriya ana dab da shawo kansu, kuma an shawo kansu, za a shawo kansu idan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shetttima ya hau."

Kara karanta wannan

Ana Gab da Babban Zabe 2023, Shugaban Jam'iyya Na Jiha Guda Ya Yi Murabus, Ya Fadi Dalili 1

- Yace.

"Za mu zabi gwamnati mai karfi da za ta kawo tsarika masu karko, masa'antu masu karko da daidaituwar tattalin arziki ga 'yan Najeriya wanda hakan zai sa su mori kasar su.
"A matsayinmu na 'yan Najeriya, ya kamata mu hadu tare matsayin kasa daya. Akwai bukatar hadin ka, mu yi watsi da kabilanci tare da banbancin addini kuma mu gane kasar ba tamu bace mu kadai.
“Akwai bukatar mu saka bukatar kasar nan a gaba. Saboda haka ne yau nake fada muku cewa ku zabi Bola Ahmed Tinubu matsayin wanda zai iya, shi ne wanda ke da gogewar kula da matsalolin da suka addabi Najeriya, kanana ko manya."

Bidiyon Tinubu ya na rawan 'Buga' bayan taron gidan Chatham

A wani labari na daban, bayan kammala taron gidan Chatham a ka gayyaci Tinubu a Landan, shi da abokan tafiyarsa sun hada wata liyafar cin abincin dare.

Gogaggen 'dan siyasan ya tashi bayan saka waka da aka yi inda ya dinga kwasar rawa cike da nishadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel