Shugaban Jam'iyar LP Na Jihar Legas, Salako, Ya Yi Murabus Kan Dalili Daya

Shugaban Jam'iyar LP Na Jihar Legas, Salako, Ya Yi Murabus Kan Dalili Daya

  • Shugaban jam'iyyar Labour Party reshen jihar Legas, Kayode Salako, ya yi murabus daga kujerarsa kan abu daya
  • Mista Salako ya bayyana cewa ya yanke shawarin sauka ne saboda ya maida hankali kan neman takarar dan majalisar tarayya
  • LP ta yi kaurin suna a Najeriya tun bayyana ayyana Peter Obi a matsayin dan takararta na shugaban kasa a 2023

Lagos - Shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na jihar Legas, Kayode Salako, ya yi murabus daga mukaminsa kwanaki kasa da 50 gabanin babban zabe.

Jigon LP yace ya dauki matakin sauka daga mukaminsa ne saboda ya nemi zama mamba a majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazabar Oshodi-Isolo I a zaben 2023.

Labour Party.
Shugaban Jam'iyar LP Na Jihar Legas, Salako, Ya Yi Murabus Kan Dalili Daya Hoto: channelstv

Salako ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Channels tv ranar Laraba, awanni bayan miƙa shugabancin LP ga tsohuwar mataimakiyar shugabar mata, Dayo Ekong.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Burtaniya ta gayyaci Atiku don wata ganawar sirri, an gano abin da suka zanta akai

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Mun zauna taron maso ruwa da tsaki a Legas jiya (Talata), bisa ra'ayin kaina na miƙa gudanar da harkokin jam'iyya ga Misis Dayo Ekong saboda ina son shiga takara."
"Ni ne dan takarar kujerar dan majalisa mai wakiltar mazabar Oshodi-Isolo I majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar LP. Ya rage saura kwanaki 40 zabe kuma ina son maida hankali na fuskanci duk wani kalubale."

Ana hasashen jam'iyyar Labour Party ka iya zama ta uku bayan manyan jam'iyyu biyu wacce mai yuwuwa ta ba da mamaki biyo bayan fitar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa.

Mista Obi na kara karbuwa musamman a wurin matasa da kuma goyon bayan da yake samu daga dattawan kasa kamar tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.

Dan takarar LP ya shiga gaban sauran takwarorinsa na jam'iyu 17 harda Atiku da Tinubu a wani zaben gwaji da aka gudanar, da yawan 'yan takara sun yi fatali da batun.

Kara karanta wannan

A Gaban Buhari a Yobe, Bola Tinubu Ya Faɗi Matakin da Zai Dauka Kan ASUU Idan Ya Ci Zaben 2023

Zan Kawo Karshen Yajin Aikin ASUU Da Zaran Na Zama Shugaban Kasa, Tinubu

A wani labarin kuma Dan takarar shugaban kasa na APC ya yi alƙawarin daidaita jami'o'in Najeriya idan ya samu nasara a 2023

A wurin Ralin APC a Damaturu, Yobe, Bola Tinubu ya sha alwashin kawo karshen yawan yajin ASUU idan ya zama magajin Buhari.

A wurin taron kamfen wanda Buhari ya halarta, tsohon gwamnan Legas yace zai baiwa daliban jami'o'in Najeriya rancen kudaɗe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel