Kotun Daukaka Kara Ta Kori 'Yar Takarar PDP a Jihar Arewa, Ta Fadi Halastacce

Kotun Daukaka Kara Ta Kori 'Yar Takarar PDP a Jihar Arewa, Ta Fadi Halastacce

  • Kotun daukaka ƙara mai zama a Abuja ta kori yar takarar PDP a mazabar tarayya Ado/Okpokwu/Ogbadibo, jihar Benuwai
  • Kwamitin Alkalai uku ya ayyana Mista Agbo a matsayin halastaccen dan takarar PDP a wannan mazaba a zaben 2023
  • An kai ruwa rana game da dan takarar majalisar tarayya a mazabar ne bayan dan majalisa mai ci ya sha kaye a zaben fidda gwani

Abuja - Kotun daukaka kara mai zama a Abuja, ranar Alhamis, ta tsige Aida Ogwuche daga matsayin 'yar takarar majalisar tarayya ta PDP mai wakiltar mazabar Ado/Okpokwu/Ogbadibo, jihar Benuwai.

Da yake yanke hukunci, kwamitin Alkalai uku karkashin mai shari'a Bature Gafai, ya ayyana Francis Agbo a matsayin halastaccen ɗan takarar PDP na mazabar a zaben watan Fabrairu.

Aida Ogwuche.
Kotun Daukaka Kara Ta Kori 'Yar Takarar PDP a Jihar Arewa, Ta Fadi Halastacce Hoto: premiumtimesng
Asali: UGC

Mista Gafai yace Mis Ogwuche na matsayin ma'aikaciyar hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) a lokacin da aka gudanar da zaben fidda gwanin PDP kuma hakan ya saba wa kundin mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban Kasa Buhari Ya Gana da Wani Dan Takara, Ya Daga Masa Hannu a Aso Rock

Premium Times ta rahoto cewa dogaro da sashi na 66 (I) (f) na kundin tsarin mulki, Kotun ɗaukaka kara da ayyana tsayar da Ogwuche a matsayin "Karya doka kuma bai inganta ba."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Hukuncin karamar Kotu na amincewa yar takarar da ake kara ta shiga zaben fidda gwani ya yi wa doka hawan kawara kuma ba daidai bane."

Bayan haka Kotun daukaka karan ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta janye Satifiket din nasara da ta baiwa Mis Ogwuche sannan ta baiwa Mista Agbo a matsayin sahihin dan takara.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Agbo, shi ne mamba mai wakiltar mazabar Ado/Okpokwu/Ogbadibo a majalisar wakilan tarayya mai ci daga jihar Benuwai.

A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2022, babbar Kotun tarayya mai zama a Makurdi ta tabbatarwa Aida Ogwuche da matsayin halastacciyar yar takarar PDP a mazabar, Sunnews ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tafiyar Peter Obi Ta Samu Tagomashi A Kaduna Yayin Da Mataimakin Kakakin Majalisa, Mamba Suka Bar APC Zuwa LP

Bisa rashin gamsuwa da Hukuncin, Agbo ya garzaya Kotun daukaka ta Abuja ya roki ta kwace takarar Ogwuche saboda ba ta yi murabus daga mukaminta na FIRS ba kwanaki 30 kafain zaben fidda gwani.

Buhari Ya Gana da Dan Takarar Gwamnan Abiya Na APC

A wani labarin kuma Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ɗaga hannun dan takarar gwamnan Abiya na jam'iyyar APC a Aso Rock

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kebe da dan takarar gwamnan Abiya a inuwar APC, Ikechi Emenike da matarsa a Aso Villa. Buhari ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takaran kuma ya ɗaga masa hannu. An ba Buhari kyautar zanen Hotonsa a 2012.

Asali: Legit.ng

Online view pixel