2023: Shaharraren Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Zai Faru A Zaben Gwamnan Katsina, Abia Da Taraba

2023: Shaharraren Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Zai Faru A Zaben Gwamnan Katsina, Abia Da Taraba

  • Primate Elijah Ayodele ya saki wasu ababe da ya hango da hasashe gabanin babban zaben shekarar 2023
  • Ya bayyana cewa za a fafata sosai a zaben gwamnan jihar Katsina ya kuma yi kira ga APC ta yi takatsantsan da PDP
  • Primate Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual ya saki hasashensa game da zabukan gwamna a jihohin Abia, Katsina da Taraba

Fitaccen malamin addinin, cikin sanarwar da kakakinsa, Osho Oluwatosin ya fitar ya ce Alex Otti na jam'iyyar Labour da Enyinnaya Nwafor na YPP suna cikin wadanda za su iya lashe kujerar gwamna na Abia.

Ya ce wadannan yan takarar za su iya cin zabe idan har sun yi shirinsu yadda ya dace.

Primate Ayodele
2023: Shaharraren Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Zai Faru A Zaben Gwamnan Katsina, Abia Da Taraba. Hoto: Photo: Primate Elijah Ayodele
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Hadimin Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Atiku, Ya Fadi Dan Takarar Da Yake Goyon Baya a 2023

Primate Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar PDP mai mulki a jihar ba za ta kai labari ba saboda rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinyewa, yayin da dan takarar APGA, Greg Ibe, ta yi wuya ya yi nasara saboda rashin lafiyarsa.

Ya ce:

"A jihar Abia, idan PDP bata yi hankali ba, za a kallubalanci dan takararta a wannan zaben. Idan dan takarar jam'iyyar Labour, Alex Otti ya yi aiki tukuru kuma ya yi shiri mai kyau, za a ji sunansa a ko ina.
"Dan takarar YPP, Injiniya Enyinnaya Nwafor shima zai iya motsi mai kyau amma dan takarar APGA, Greg Ibe, ba zai iya tabuka komai ba saboda rashin lafiya da na ke ganin za ta kama shi."

A jihar Taraba kuma, Primate Ayodele ya ce dan takarar PDP, Kefas Agbu, yana hanyar yin nasara, yayin da ya ce jam'iyyar ta PDP kuma za ta ci zaben shugaban kasa a jihar.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bude Baki Ya Saki Maganganu, Ya Fadi Yadda Atiku Ya Samu Takara a PDP

Ya ce:

"Dan takarar PDP na Taraba, Kefas Agbu zai yi nasara ko a wane hali kuma zai tabuka abin a zo a gani. PDP za ta ci Taraba a zaben gwamna da shugaban kasa."

Hasashensa game da jihar Katsina kuma kamar yadda PM News ta rahoto, ba zai yi wa jam'iyyar APC dadi ba.

Primate Ayodele ya bayyana cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP zai tada kura a zaben gwamnan ya kuma gargadi jam'iyyar APC ta yi taka-tsantsan.

Ya ce:

"A Katsina, idan ba wani ikon Allah ba, idan ba a kula ba kuma idan ba anyi magudi ba, za a iya yaudarar dan takarar APC kuma ba za su zabe shi ba."

Malamin Addini Ya Yi Hasashe Game Da Zaben 2023

A baya, shugaban na cocin INRI, Elijah Ayodele ya gargadi, Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC gama da zaben na 2023.

Kara karanta wannan

Rigingimun PDP: Daga Karshen Atiku Ya Sake Rokon Gwamnanonin G5

Jaridar PM News ta rahoto cewa Primate Ayodele ya fada wa Yakubu kada ya sake ya bari yan siyasa su yi masa katsalandan cikin harkokin hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel