2023: An Yi wa Atiku Iyaka Wajen Neman Mulki, An hana Shi Yin Kamfe a Jihar PDP

2023: An Yi wa Atiku Iyaka Wajen Neman Mulki, An hana Shi Yin Kamfe a Jihar PDP

  • Kwamitin da ke da alhakin tallata takarar Alhaji Atiku Abubakar yana fama da kalubale a Ribas
  • Ana tunanin ba a bada dama Atiku Abubakar ya yi amfani da wani wuri domin yin kamfe a jihar ba
  • Gwamnatin Nyesom Wike ta yarda masu takaran Majalisa, Sanatoci da Gwamna a PDP suyi kamfe

Rivers - Masu yi wa Alhaji Atiku Abubakar yakin neman zama shugaban Najeriya a 2023, ba su da damar shiga bainar jama’a domin suyi kamfe a Ribas.

The Nation ta rahoto kwamitin yakin zaben Atiku Abubakar a jihar Ribas ta bakin Ogbonna Nwuke yana cewa sun samu izinin kamfe daga gwamnati.

Ogbonna Nwuke ya ce sun biya kudin da ake bukata domin tallata ‘yan takaran PDP a zabukan majalisar dokoki da tarayya da Sanatoci da na Gwamna.

Kara karanta wannan

An Bayyana Jihar da Ake So Ta fi Kawowa Tinubu/Shettima Kason Kuri’u a Najeriya

Ko da cewa Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ribas ta biya N95m domin samun wurin yin taron kamfe, gwamnati tayi mata kaidi da shiga wasu wuraren.

Wike ya biya kudin kamfe

Amma jam’iyyar mai mulki ta ce ta samu damar da za tayi amfani da makarantu wajen yawon yakin neman zaben da za ayi a watan Fubrairun nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce Mai girma Nyesom Wike ya biya wadannan kudi kamar yadda gwamnatinsa tayi wata doka na musamman a game da yakin zabe.

'Yan PDP
Magoya bayan PDP a Katsina Hoto: Atiku Abubakar, @Atiku.org
Asali: Facebook

Ana cewa kudin da aka biya na yi wa sauran ‘yan takaran PDP kamfe ne, ban da Atiku Abubakar mai neman zama shugaban kasar Najeriya a bana.

Wike yana cikin kungiyar G5 na gwamnonin PDP da ke yakar tikitin Atiku/Okowa. Wani rahoto ya ce har yanzu Atiku bai da damar yin kamfe a Ribas.

Kara karanta wannan

Ana dab da zabe: Alkali ya sa a kamo masa dan takarar gwamnan PDP a wata jiha

Sharadin da Gwamnati ta bada

Dokar da Gwamnan na Ribas ya yi ta ce duk mai neman yin amfani da makarantar gwamnati domin kamfe sai ya rubuta takarda ga kwamishinar ilmi.

Baya ga haka za a biya N5m da za ayi amfani da su wajen gyaran makarantar bayan taron.

Kwamishinan ilmin Ribas, Farfesa Chinedum Mbom ya tabbatar da ya karbi takardar PDP da shaidar kudin da suka biya, an amince su yi kamfe a makarantu.

Fasto ya zama 'Dan takarar Gwamna

Rahoto ya zo a makon nan cewa Limamin cocin katolikan da ya zama 'Dan takarar Gwamna, ya jero abubuwa 7 da zai yi idan aka aka zabe shi a Jihar Benuwai

Faston da ke takarar Gwamnan Benuwai a Jam’iyyar APC, Rev. Fr. Hyacinth Alia ya gabatar da manufofin da yake tafe da su, na farko shi ne kare al’ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel