Zaben 2023: Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Kwankwaso Da Obi Ke Yi Wa Tinubu Aiki
- Bulaliyar majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce Rabiu Kwankwaso dan takarar shugaban kasa na NNPP da Peter Obi na LP na yi wa Bola Tinubu aiki a zaben 2023
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce yan takarar shugaban kasar biyu na yi wa Tinubu aiki ne a kaikaice don sun raba kuri'un sauran yankunan kasar amma banda yankin da APC ta fi magoya baya
- Kalu ya ce yankin da APC ta fi samun magoya baya sune arewa maso gabas da arewa maso yamma kuma har yanzu magoya bayan na APC na nan daram-dam
Gabanin babban zaben shekarar 2023, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce yana da kwarin gwiwa sosai cewa magoya bayan jam'iyyar APC a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas suna nan daram-dam.
Bulaliyar majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, 10 ga watan Janairu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanata Kalu ya kuma ce dan takarar shugaban kasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso da takwararsa na jam'iyyar Labour (LP) na yin aiki don nasarar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu 'aiki' a kaikaice.
Ban yarda da zabukan jin ra'ayin da ake yi kafin zabe ba, in ji Kalu
Sanata Kalu ya kuma ce bai yarda da zabukan jin ra'ayin mutane da ake yi ba gabanin zabe da wasunsu ke nuna cewa Obi na gaba da Tinubu da sauran yan takarar shugaban kasa.
Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce an yi zaben jin ra'ayin ne tsakanin manyan mutane kuma hakan ba ya nuna ainihin abin da yan Najeriya ke tunani game da zaben.
Kalamansa:
"Ban yarda da zaben jin ra'ayin al'umma ba; ba gaskiya zabukan ne nunawa ba.
"Idan gaskiya zaben ke nunawa, Kwankwaso da Peter suna mana aiki ne domin babu wanda ya taba yankin magoya bayanmu; babu wanda ya taba inda APC ta fi karfi. Arewa maso yamma da arewa maso gabas ne masoyanmu suka fi yawa.
"Amma idan ka zo Kudu maso gabas, kansu a rabe ya ke, idan ka zo kudu maso kudu, a rabe ya ke, Obidients sun cinye yankin. Babu wanda ya taba yankin mu; bangaren mu na nan daram-dam; babu abin da ya taba shi."
Gwamna Ganduje: Arewa ba ta da dalilin rashin zaben Asiwaju Bola Tinubu
A wani rahoton daban, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce mutanen arewa ba su da wani dalilin rashin zaben dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwajub Ahmed Tinubu a 2023.
Ganduje ya ce Tinubu ya taka muhimmiyar rawa wurin ganin cewa Shugaba Buhari ya yi nasarar zama shugaban kasa, don haka lokaci ya yi da za a masa sakayya.
Asali: Legit.ng