IPOB: Fitaccen Sanatan APC Ya Ce A Shirye Ya Ke Ya Tsayawa Nnamdi Kanu Beli, Ya Bayyana Dalilinsa

IPOB: Fitaccen Sanatan APC Ya Ce A Shirye Ya Ke Ya Tsayawa Nnamdi Kanu Beli, Ya Bayyana Dalilinsa

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya ce a shirye ya ke ya karbi belin Mazi Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyar kungiyar IPOB, masu son kafa Biafra
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce yana da alaka mai kyau da iyalan Nnamdi Kanu kuma ba zai yi watsi da su a wannan halin da suke ciki ba
  • Jigon na APC ya ce yana kyautata zaton gwamnatin tarayya za ta bi umurnin kotu kan bukatar neman bada belin Kanu, shi kuma zai ajiye shi a gidansa idan yana so

Sanata Orji Kalu ya ce a shirye ya ke ya tsayawa Nnamdi Kanu, shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, idan gwamnati za ta bada belinsa.

Babban bulaliyar majalisar dattawan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga watan Janairu, lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Sanatan APC Ya Bayyana Yadda Kwankwaso Da Obi Ke Yi Wa Tinubu Aiki

Orji Kalu da Kanu
Fitaccen Sanatan APC Ya Ce A Shirye Ya Ke Ya Tsayawa Nnamdi Kanu Beli, Ya Bayyana Dalilinsa. Hoto: Photo credits: Senator Orji Uzor Kalu, Kingsley John Chibuzor
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

"Zan tsaya masa (Kanu) idan gwamnatin tarayya tana son bani shi."

FG za ta bi umurnin kotu kan Nnamdi Kanu, In Ji Kalu

Sanata Kalu, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce yana kyautata zaton cewa gwamnatin tarayya za ta bi umurni kotu game da belin shugaban na IPOB.

Jigon na jam'iyyar APC ya ce yana da kusanci da iyalan Kanu a Abia amma shugaban na IPOB da yan uwansa ba su saurari shawararsa ba.

Amma, ya ce ba zai iya watsi da iyalan Kanu ba a wannan lokacin da suke da matsala da gwamnatin Najeriya.

Kalu ya ce:

"Na na nada mahaifinsa sarkin garinsu lokacin da na ke gwamna. Ina da kusanci da su amma ba su saurare ni ba amma hakan ba zai sa in yi watsi da su ba. Ba zan yi watsi da su ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban Kasa Mai 'Rowa' Najeriya Ke Buƙata, In Ji Peter Obi

"Zan tsaya masa idan gwamnatin tarayya na son sakinsa. Kuma zan ajiye shi a gidan na a Abuja ko Igbere (a Abia) kuma in bashi shawara."

Nnamdi Kanu na fama da ciwon hanji, lafiyarsa na kara tabarbarewa, in ji lauyansa

A wani rahoton, kun ji cewa lafiyan shugaban kungiyar Biafra, Nnamdi Kanu na kara tabarbarewa yayin da ya ke tsare a hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.

Ifeanyi Ejiofor, lauyan Kanu ya bayyana cewa shugaban na IPOB ba shi da lafiya, yana fama da cututtuka masu yawa har da cutar olsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel