Abin da Ya Jawo Jami’ai Suka Ragargaji Hadimin Abba Gida Gida Inji Yaron DG DSS

Abin da Ya Jawo Jami’ai Suka Ragargaji Hadimin Abba Gida Gida Inji Yaron DG DSS

  • An samu sabani tsakanin mai dakin Darekta Janar na DSS da ‘dan takaran NNPP a filin jirgin sama
  • Abba Yusuf Bichi ya ce matar shugaban hukumar DSS ba ta umarci a cafke Abba Kabir Yusuf ba
  • ‘Dan wasan kwallon ya zargi Gida Gida da cin mutuncin Aisha Yusuf Bichi, har abin ya zama fada

Abuja - Abba Yusuf Bichi wanda mahaifinsa yake rike da kujerar shugaban hukumar DSS na Najeriya, ya yi magana a kan wasu rahotanni da ke yawo.

A farkon makon nan aka rika yada labari cewa an samu takaddama tsakanin matar shugaban DSS da ‘Dan takarar Gwamna a Kano, Abba Kabiru Yusuf.

Abba Yusuf Bichi ya yi amfani da shafinsa na Twitter, ya bada na shi bangaren labarin rigimar, ya yi magana ne a daren yau ta @Abba_YusufBichi.

Kara karanta wannan

Mahadi Shehu Ya Fede Obasanjo, Ya Tona Boyayyar Hikimar Goyon Bayan Peter Obi

A cewarsa, mai dakin shugaban hukumar DSS ba ta umarci jami’an tsaro na fararen kaya su cafke Abba Kabiru Yusuf wanda ake kira Abba Gida Gida ba.

Haka zalika, matashin ya ce Aisha Yusuf Bichi ba ta umarci a kashe hadimin ‘dan takaran ba. An ga hotunan Garba Kilo da alamar yi masa jina-jina.

Abba Gida Gida
Abba Kabiru Yusuf (Abba Gida Gida) Hoto: @hallirunazeer
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar Abba Yusuf Bichi a Twitter

"‘Yan daban Abba Gida Gida ne suka tare tawagar motocin Mai dakin Darekta Janar na DSS, sai jami’an DSS su ka nemi shiga filin jirgi, amma suka hana su.
Jami’an tsaron sun tunkare su, amma sai ‘yan daban suka tada rigima, yayin da duk ake yin wannan, Abba Gida Gida yana zaune cikin motarsa yana kallo!
Da DSS suka sake yunkurin shiga filin tashin jirgin, sai Abba (Gida-Gida) ya fito, yana cin zarafin jami’an, sannan ya umarci ‘yan dabansa su tada rigima.

Kara karanta wannan

Munanan Bayanai Sun Bullo a kan Dalilin Cafke Mutumin Atiku da Aka Yi a Kasar Ingila

Bayan ganin abin da yake faruwa, sai mai dakin Darekta Janar ta sauko daga motarta, ta roki Abba Gida Gida, sai ya koma kan motar, ya shiga zaginta.
Daga nan wani daga cikin ‘yan dabansa ya nemi ya aukawa matar DG, a nan ne jami’an DSS da ke tsaron ta suka maida martani, har ya samu rauni.”

- Abba Yusuf Bichi

Atiku ya zauna da Manoman Arewa

An ji labari tsohuwar kwamishinar noma a jihar Kano, Baraka Sani ta tara manoman Arewa maso yamma, ta fada masu su zabi Atiku Abubakar a 2023.

Dr. Baraka Sani tayi kira da babbar murya ga manoman su zabi jam'iyyar PDP domin a magance matsalolin noma da ake fama da su a yankin Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel