Boyayyun Bayanai Sun Fito Kan Rikicin Siyasar da Ya Jawo Tsige Wazirin Bauchi

Boyayyun Bayanai Sun Fito Kan Rikicin Siyasar da Ya Jawo Tsige Wazirin Bauchi

  • Masarautar Bauchi ta sauke Muhammadu Bello Kirfi daga sarautar da yake kai na Wazirin Bauchi
  • Fada ta zargi Alhaji Muhammadu Bello Kirfi da rashin da’a ga Gwamnatin Bala Mohammed
  • Amma ana tunanin rashin jituwa tsakanin Waziri da Gwamna Bala ne ya jawo ya rasa rawaninsa

Bauchi - Sababbin bayanai sun bullo a game da dalilin da ya sa masarautar Bauchi ta cirewa Alhaji Muhammadu Bello Kirfi rawanin Wazirin Bauchi.

Abin da masarautar ta shaidawa Duniya shi ne tsohon Wazirin bai yi wa Gwamnatin jihar Bauchi biyayya, Daily Trust ta ce abin yana da alaka da siyasa.

Muhammadu Bello Kirfi ya rike Minista a gwamnatin Shehu Shagari da Olusegun Obasanjo, kuma yana cikin manyan magoya bayan jam’iyyar PDP.

Kwanakin baya tsohon Wazirin na Bauchi ya kira taron masu ruwa da tsaki a jihar, ya umarce su da su taya Atiku Abubakar yakin neman zaben bana.

Kara karanta wannan

Ba Don Shugaba Buhari Ba, Da Tuni Jihata Ta Tarwatse, Gwamna Ya Fayyace Gaskiya

Kirfi ya fita daga batun Bala?

Bello Kirfi ya fadawa mutanensa su goyi bayan Atiku ne kurum, ya yi watsi da batun takarar Bala Mohammed wanda yake kokarin zarcewa a kan mulki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wazirin Bauchi
Sallar idi a fadar Sarkin Bauchi Hoto: 247ureports.com
Asali: UGC

Wata majiya a dangin dattijon ta shaidawa jaridar cewa rikicin Waziri da Gwamna ta samo asali ne tun shekarar bara da Bala zai fito takarar shugaban kasa.

Mai girma gwamnan ya tuntubi Bello Kirfi a kan batun neman tikitin jam’iyyar PDP, sai Waziri ya ba shi shawara ya hakura, ya janyewa Wazirin Adamawa.

Bala Mohammed bai ji dadin shawarar nan da Wazirin Bauchi na wancan lokaci ya ba shi ba. Majiyar ta ce wannan ne silar tsamin alakar, har ta kai ga haka.

Taron Waziri da mutanensa a Bauchi

Da Kirfi ya zauna da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 20 a karshen 2022, ya fada masu bai yanke shawara a kan ‘dan takararsa na Gwamna ba.

Kara karanta wannan

Sarkin Bauchi ya Tsige Mutumin Atiku daga Sarautar Waziri a Dalilin Rikici da Gwamna

Waziri yana cikin masu juya siyasar jihar Bauchi, ya taka rawar gani wajen zaben Bala a 2019.

A dalilin haka ne aka ba 'dansa, Yakubu Bello Kirfi kujerar Kwamishina, ko da aka sauke shi sai aka dauko ‘yaruwarsa, Saadatu Bello Kirfi

Mai magana da yawun Gwamna, Mukhtari Gidado ya ki cewa uffan a kan lamarin. Rahoto ya zo Muhammad Uba Ahmed zai zama sabon Wazirin Bauchi a yau.

'Diyar Waziri ta bar gwamnatin Bala

Labari ya zo cewa Hajiya Sa'adatu Bello Kirfi, ta rubuta wasikar murabus daga mukaminta, yanzu ta sauka daga matsayin kwamishina a jihar Bauchi.

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Mohammed na jihar ya bada umarnin a tsige mahaifinta daga sarautarsa ta Wazirin Bauchi kan zargin rashin biyayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel