An Bayyana Jihar da Ake So Ta fi Kawowa Tinubu/Shettima Kason Kuri’u a Najeriya

An Bayyana Jihar da Ake So Ta fi Kawowa Tinubu/Shettima Kason Kuri’u a Najeriya

  • An rantsar da kwamitin da zai yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima aiki a Yobe
  • Ahmad Ibrahim Lawan ya yi jawabi wajen bikin rantsarwar da aka yi a gidan gwamnati a Damaturu
  • Shugaban majalisar dattawan yace akalla 98% suke yi wa Tinubu hari a zaben watan Fubrairun nan

Yobe - Ahmad Ibrahim Lawan ya sha alwashin cewa jihar Yobe za ta ba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima 98% na kuri’unsu a zabe.

Rahoton Vanguard ya nuna Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana wannan ne a wajen kaddamar da kwamitin yakin neman zaben APC a Yobe.

Da yake magana a garin Damaturu a karshen makon nan, shugaban majalisar dattawan ya nuna jiharsa ta Yobe abin alfaharin jam’iyyar APC ce.

Ahmad Lawan yake cewa za suyi duk abin da ya dace wajen ganin APC ta samu nasara. Jawabin shugaban majalisar ya fito ta bakin Ola Awoniyi.

Kara karanta wannan

Manyan Dalilai Uku da Zasu Ja Hankalin 'Yan Arewa Su Zabi APC a 2023, Gwamna

An nada kwamiti mai karfi a Yobe

Mai taimakawa shugaban majalisar wajen yada labarai ya ce tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam da Ahmad Lawan za su jagoranci kwamitin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Leadership ta ce Sanata Bukar Abba Ibrahim zai zama uba na kwamitin neman zaben.

'Yan APC
Taron yakin neman zaben APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Maganar da Ahmad Ibrahim Lawan ya yi

"Kamar yadda shugaban kwamitin yakin zabe ya fada, za mu aiki tukuru wajen tabbatar da cewa jam’iyyar nan ta APC ta lashe duka kujeru da yardar Allah.
Za muyi aiki babu gajiya wajen tabbatar da cewa sai inda karfinmu ya kare, za muyi duk abin da ake bukata domin jihar Yobe abin alfaharin jam’iyyar APC ce.
A dalilin haka, ba za mu bari ‘yan jam’iyyar APC su ji kunya ba.
Mun yarda za muyi galaba a zaben shugaban kasa idan ana batun aiki. Za mu iya zama wanda suka fi kowa bada yawan kason kuri’u kamar yadda muka saba.

Kara karanta wannan

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

Ba mu harin kasa da 98% ga ‘dan takaran kujerar shugaban kasar mu.

- Ahmad Lawan

La’akari da takarar Shettima, Sanata Lawan ya ce ya zama dole ‘Yan Yobe su hada-kai, hakan zai sa duk wani wanda ya tsaya takara a APC ya ci zabe.

APC ta rasa mabiya a Kano

Rahoto ya zo kwanaki cewa wasu Bayin Allah da suka je kallon ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu a Kano sun tafi barzahu a sanadiyyar wani hadarin mota.

Sanatan Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Kabiru Gaya ya halarci sallar jana'izar da aka yi wa wadanda suka riga mu gidan gaskiya a kwanar 'dan gora.

Asali: Legit.ng

Online view pixel