2023: Kwankwaso Ya Samu Tagomashi Mai Ban Mamaki A Yayin Da Tsaffin Ciyamomin PDP Da Kansila Suka Shigo NNPP

2023: Kwankwaso Ya Samu Tagomashi Mai Ban Mamaki A Yayin Da Tsaffin Ciyamomin PDP Da Kansila Suka Shigo NNPP

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta samu karuwa na tsaffin ciyamomi da kansila a jihar Gombe
  • Daga cikin wadanda suka fice daga PDP suka koma NNPP din a baya-bayan nan akwai tsaffin ciyamomi na kananan hukumomin Billiri, Kwami da Nafada
  • Saura sun hada da tsohon da tsohon kansila daga mazabar Tal da ke karamar hukumar Billiri daga shekarar 2013 zuwa 2015

Jihar Gombe - A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, na cigaba da samun sabbin mambobi daga jam'iyyun APC da PDP.

A wannan lamarin na baya-baya, tsaffin shugabannin kananan hukumomi hudu daga Billiri, Kwami da Nafada da tsohon kansila sun fita daga PDP sun shiga NNPP.

Kwankwaso
2023: Kwankwaso Ya Samu Tagomashi Mai Ban Mamaki A Yayin Da Tsaffin Ciyamomin PDP Da Kansila Suka Shigo NNPP. Hoto: (Photo: @KwankwasoRM)
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

2023: Ana Zaman Jiran Zabin G5, Atiku da PDP Sun Yi Babban Kamu a Jihar da APC Ke Mulki

Sun shiga NNPP din ne bayan taro da dan takarar gwamna na NNPP a babban zaben shekarar 2023 da ke tafe.

The Punch ta rahoto cewa daga cikin wadanda suka sauya shekan akwai mataimakin ciyaman na karamar hukumar Billiri (2003), Philip Bataliya, da Yila Dankuka, wanda ya rike wannan mukamin daga 2013 zuwa 2015.

Saura sun hada da tsohon shugaban karamar hukumar Kwami, Auwalu Rabiu Daba, tsohon ciyaman na karamar hukumar Nafada, Aliyu Idris Biri, da tsohon kansila daga mazabar Tal da ke karamar hukumar Billiri daga 2013 zuwa 2015.

An tattaro cewa sabbin mambobin na NNPP za su yi aiki tukuru domin ganin yan takarar jam'iyyar ta NNPP da dan takarta na shugaban kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sunyi nasara a 2023.

Shugabancin kasa na 2023: Kwankwaso ya bayyana matsayinsa na karshe kan janyewar takara

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana wadanda ke baza jita-jitar majarsa da wata jam'iyya a matsayin yan siyasa marasa madafa.

Kara karanta wannan

2023: 'Dan Majalisa Dan Gani Kashenin Kwankwaso Ya Fice Daga NNPP, Ya Koma Jam'iyar Da Ya Fito

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba yayin da ya ke magana da manema labarai a Abeokuta bayan ya gama jawabi ga mambobin NNPP a sakatariyar jam'iyyar da ke babban birnin jihar.

Dan takarar shugaban kasar na NNPP ya karyata cewa yana shirin yin maja da wata jam'iyya ko dan takara gabanin babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164