Allah Bai Sanar Dani Wanda Zai Gaji Buhari a Zaben 2023 Ba, Inji Fitaccen Faston RCCG, Adeboye

Allah Bai Sanar Dani Wanda Zai Gaji Buhari a Zaben 2023 Ba, Inji Fitaccen Faston RCCG, Adeboye

  • Babban malamin coci ya bayyana kadan daga abin da yake bukata mabiyansa su yi a zaben 2023 mai zuwa
  • Fasto Adeboye ya ce Allah bai sanar dashi wanda zai gaji Buhari ba a zaben da ke tafe nan kusa
  • ‘Yan siyasa na ci gaba da bayyana matsayarsu da kuma tallata ‘yan takara gabanin babban zaben 2023

Jihar Ogun - Babban malamin cocin Redeemed, fasto Enoch Adeboye ya bayyana cewa, har yanzu Allah bai sanar dashi wanda zai zama shugaban kasan gobe ba a zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Malamin ya bayyana hakan ne da sanyin safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Janairu a wani babban taron addini da ya gudanar a Redemption City da ke kan babban titin Legas-Ibadan a jihar Ogun.

Adeboye ya kuma bayyana cewa, ya kamata mambobin cocin na RCCG da ma dukkan ‘yan Najeriya su tabbatar suna rike da katin zabensu a hannu on kada kuri’u.

Kara karanta wannan

2023: Na Hannun Daman Atiku Ya Bayyana Bayanai Masu Muhimmanci Kan Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Sha Kaye

Adeboye ya yi magana game da shugaban Najeriya na gaba
Allah Bai Sanar Dani Wanda Zai Gaji Buhari a Zaben 2023 Ba, Inji Fitaccen Faston RCCG, Adeboye | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Kowa ya koma ga Allah, a mallaki katin zabe

A cewarsa, kamata ya yi ‘yan kasar su yi zabe idan Allah ya sanar dasu shugaba na gaba da kuma idan bai sanar dasu ba, Daily Post ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Za ku iya cewa zaben na tafe a wata mai zuwa kuma bai yi magana ba har yanzu. Ina ba da shawarin ku kakkabe katin zabenku ku kasance cikin shiri.
“Idan bai yi magana ba kafin zabukan, to sai ku yi zabe daidai da abin da zukatanku suka natsu dashi. Idan ya fada mani, shikenan, zan iya fada muku ko kuma akasan haka.”

Da yake magana a gaban dandazon jama’a game da hasashen me zai faru a zaben, Adeboye ya ce yana da matukar muhimmanci mutane suke sauraran abin da Allah ya sanar da bayinsa na kirki ba masu hasashen karya ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Magantu Kan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Shugaban na cocin RCCG ya kuma kara da cewa, mutanensa su zama masu rayuwa da tsayawa ga kalaman ubangiji, kuma su yi na’am da mulkinsa da kaddararsa.

Dalilin da Yasa Gwamnonin APC Na Arewa Ke Son Tinubu Ya Gaji Buhari a Zaben Bana

A wani labarin kuma, gwamnonin Arewacin Najeriya na kaunar Tinubu ya gaji Buhari a zaben 2023 saboda mika mulki zuwa Kudancin Najeriya.

Wannan na fitowa ne ta bakin gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule yayin da aka yi wani taron siyasa a jiharsa.

Ana ta yada jita

-jitan cewa, akwai wasu gwamnonin Arewa 11 na APC da ke aiki a boye don ganin Atiku ya gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel