Zagi Da Suka Ba Zai Hana Ni Goyon Bayan Wanda Nake So A 2023 Ba, Wike

Zagi Da Suka Ba Zai Hana Ni Goyon Bayan Wanda Nake So A 2023 Ba, Wike

  • Ga dukkan alamu gwamna Wike ya yanke cewa ba zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ba a zabe mai zuwa
  • Gwamnan jihar Ribas ya ce duk wani zagin da za'a masa ba zai sa ya sauya abinda ya kudiri aniyar yi ba
  • Wasu rahotanni sun ce tawagar G5 zasu bayyana dan takarar da zasu mara wa baya ranar Alhamis, 5 ga watan Janairu, 2023

Rivers - Yayin da ake tunkarar babban zaben 2023, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yace zagi da hantara ba zasu sa ya ja da baya ba game tallata dan takarar shugaban kasan da ya kwanta masa a rai.

Gwamnan, wanda ke jagorantar tawagar gaskiya watau G5 ya fadi haka ne a wurin kaddamar da fara gina Titin da ya hada Akpabu-Egbeda-Omoku a karamar hukumar Emohia ranar Laraba 4 ga watan Janairu, 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mata Za Su Samu Kudi a Karkashin Gwamnatin Mijina, In ji Matar Obi

Gwamna Wike na jihar Ribas.
Zagi Da Suka Ba Zai Hana Ni Goyon Bayan Wanda Nake So A 2023 Ba, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike yace zai maida hankali wurin tattara magoya baya ga dan takarar da zai marawa baya maimakon ya tsaya yana kace-nace da masu neman dauke masa hankali.

A kalamansa, gwamna Wike yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Idan kun so ku ci gaba da yaɗa maganganu cewa ina wa wane da wane aiki, matsalarku ce, ku ce bana tare da wane da wane duk dai ku ta shafa."
"Haka ba zai girgiza ni ko ya sa na sauya abinda ke zuciyata ba game da inda muka dosa, ina fatan kun fahimce ni? Saboda haka idan sun so su cigaba da yada jita-jita, shiyasa ma aka kirkiri kalmar jita-jita."

Muna kokarin samun kuri'un jama'a - Wike

Gwamna Wike ya kara da cewa a lokacin da yan adawa ke zaginsa, shi da yan tawagarsa sun shiga da'irar siyasa suna tattauna wa da al'umma tare da rokon samun kuri'unsu ranar zabe.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta Aike wa da Ƙani Gidan Maza Kan Soyayya da Matar Aure

Yace tuni mutane suka farga, 'yan siyasan da suka zuba masu aiki a kasa suka kawo masu ci gaba ne zasu samu kuri'unsu.

"Muna nan muna magana da al'umma, su kuma suna can yawo Radiyo da Talabijin yayin da mu kuma muke tare da jama'a, da zaran mun gama da su, lokaci ya kure."

A wani labarin kuma Tsohuwar Minista Tace Rikicin tawagar G5 ba ta shafi Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa ba

Olajumoke Akinjide tace duk wannan kace-nace da kai kawon da ake a PDP tsakanin G5 ne da shugabancin jam'iyya na ƙasa.

Olajumoke ta ba da tabbacin cewa cikin ruwan sanyi zasu shawo kan rigingimun da suka dabaibaye babbar jam'iyyar adawa a matakin ƙasa kafin zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel