Gwamna Adeleke da Wasu ’Yan Takarar Gwamna 2 Sun Ki Halartar Kaddamar da Kamfen PDP a Oyo

Gwamna Adeleke da Wasu ’Yan Takarar Gwamna 2 Sun Ki Halartar Kaddamar da Kamfen PDP a Oyo

  • Yayin da aka kaddamar kamfen PDP a jihar Oyo, gwamna Adeleke bai halarta ba saboda wasu dalilan ba a bayyana ba
  • Hakazalika, ‘yan takarar gwamna biyu a yankin Kudu maso Yamma sun ki halartar taron mai muhimmanci
  • Ana ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP, lamarin da ke tsinka ran Atiku Abubakar

Ibadan, jihar Oyo - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun bai samu halartar kaddamar da kamfen jam’iyyar PDP ba a jihar Oyo gabanin babban zaben 2023 da ke tafe nan da kwanaki, Tribune Online ta ruwaito.

Hakazalika, ‘yan takarar gwamnan PDP a jihar Ogun, Oladipupo Adebutu da Oladije Adediran (Jandor) na jihar Legas su ma basu halarci wannan taro ba da aka yi a ba dakin taro na Mapo da ke birnin Ibadan a yau Alhamis 5 ga watana Janairu.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Gwamna Wike Ya Aike Da Sabon Muhimmin Sako Ga APC da Wasu Jam'iyyu

Idan za ku iya tunawa, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo bai halarci taron rantsar da gwamna Ademola Adeleke ba a matsayin gwamna na shida da aka zaba a jihar Osun kuma gwamna na biyu a APC a jihar a zaben 2022 da ya gabata.

An yi taron PDP, masu kishin Atiku sun ki halarta
Gwamna Adeleke da Wasu ’Yan Takarar Gwamna 2 Sun Ki Halartar Kaddamar da Kamfen PDP a Oyo | Hoto: oyoinsight.com
Asali: UGC

Rikicin PDP da gwamnonin G-5 masu adawa da Atiku da Ayu

Makinde na daya daga cikin gwamnoni biyar da ke adawa da takarar Atiku da kuma wani yanki na shugabancin jam’iyyar PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran takwarorin Makinde da ke kada hantar Atiku sun hada da Nyesom Wike na jihar Ribas, Samuel Ortom na jihar Benue, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu da Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

Sai dai, rashin Adeleke a wannan taron da ma ‘yan takarar da aka ambata a Kudu maso Yamma an ce ba zai rasa nasaba da rikicin da ke kara dumama a PDP ba, OyoInsight ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Gwamna ya fadi dalili 1 da yasa gwamnonin APC a Arewa ke son Tinubu

Dalilin da yasa gwamnonin APC a Arewa ke son Tinubu ya gaji Buhari

A bangare guda, gwamnonin Arewa na APC basu da matsala da dan takararsu na shugaban kasa, kamar yadda daya daga cikin gwamnonin ya bayyana.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa, gwamnonin APC a Arewa na kaunar Tinubu ne saboda suna son mulkin Najeriya ya koma Kudancin kasar.

An yi ta cece-kuce tun bayan da aka ba Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, kana ya zabo abokin takara Musulmi daga Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel