Tinubu ya Gwada Gwanintarsa a Fannin Rawa Yayin da Dandazon Jama’a Suka Tare shi a Kano

Tinubu ya Gwada Gwanintarsa a Fannin Rawa Yayin da Dandazon Jama’a Suka Tare shi a Kano

  • Bola Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar APC a ranar Laraba ya ziyarci jihar Kano inda ya gana da dandazon magoya bayansa
  • Tsabar farin cikin da tsohon gwamnan Legas din ya shiga yasa ya kasa jawabi amma yace rawa kawai yake so ya fara da ita
  • Bayan cashewa tare da girgijewa, Bola Tinubu ya sha alwashin bautawa 'yan Najeriya tare da kawo zaman lafiya mai dorewa

Kano - ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa ta jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya kasa boye farin cikinsa kan gagarumar gayyar jama’a da suka taru a Kano yayin ralin jam’iyyar mai mulki a ranar Laraba.

Tinubu a Kano
Tinubu ya Gwada Gwanintarsa a Fannin Rawa Yayin da Dandazon Jama’a Suka Tare shi a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Legas din bayan ganin taron jama’a da suka cika wurin ralin, ya fara kwasar rawa inda ya bayyanawa jama’a cewa

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

“abu daya kadai da nake son yi shi ne rawa. Ina bukatar kida”

kuma daga bisani ya cigaba da rawansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan nan, ya sanar da gayyar jama’a cewa zai kiyaye alkawurran da yayi wa ‘yan Najeriya kuma daya daga cikin alkawurran shi ne zai samar da zaman lafiya ga iyalai.

"Zan bauta muku tare da Najeriya.”

Yayin jawabinsa, Gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, wanda shi ne shugaban zauren gwamnonin jam’iyyar APC, ya musanta rahotannin dake yawo na cewa wasu daga cikin gwamnonin APC suna ganawa ta gefe da ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Yace akasin rahotannin, dukkan gwamnonin APC suna bayan Tinubu yayin da suke tsaye tun kafin ya samu takarar shugabancin kasa.

Ya kara da cewa gwamnonin APC na yanzu da wadanda suka gabata su ne shugabannin tawagar kamfen din Tinubu kuma hakan shaida ne ta yadda suka bayyana a Kano.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

“Muna kira ga jama’ar mu da su yi watsi da dukkan labaran bogi da ke cewa gwamnonin APC suna ganawa da su.”

- Ya kara da cewa.

Hassada Obasanjo ke wa Buhari, Fadar Shugaban kasa

A wani labari na daban, fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ayyana jawabin da Cif Olusegun Obasanjo yayi na sabuwar shekara da tsabar hassada da yake wa shugaban kasan Najeriyan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel