Kwankwaso Ya Fayyace Yadda NNPP Za ta bi Wajen ba Mutane Mamaki a Zaben Fubrairu

Kwankwaso Ya Fayyace Yadda NNPP Za ta bi Wajen ba Mutane Mamaki a Zaben Fubrairu

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayanin yadda yakin kamfen yake tafiya, ya ce su za suyi nasara
  • ‘Dan takaran na NNPP a zaben bana ya nuna yana gaban Peter Obi, don haka ya ki janye masa
  • Kwankwaso ya ce ya shiga garuruwa da-dama, yana ta ganawa da talakawa domin ya lashe zabe

Abuja - BBC Hausa ta zauna da Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a zaben bana a inuwar jam’iyyar hamayyar nan ta NNPP.

‘Dan takaran ya bayyana cewa kamfen da suke yi yana tafiya daidai, domin jam’iyyar NNPP ta shiga shiyyar Arewa maso yamma da wasu yankunan kasar.

A ‘yan kwanakin nan, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya raba tutoci, kuma ya zauna da talakawa domin fahimtar matsalolin mutane a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Maidawa Obasanjo Martani a Kan ‘Dan Takaran da Yake Goyon Baya

A cewar ‘dan takaran, ya yi jawabi a wurare, ya tallata manufofinsa musamman na gyaran makarantun firamare da maida jarrabawan SSCE kyauta.

Me ya hana shi janyewa Peter Obi

Rabiu Kwankwaso ya yi bayanin abin da ya sa ya ki yin hakuri ya sallamawa Peter Obi tikitin shugaban kasa domin su tunkari jam’iyyun APC da PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

‘Dan siyasar yake cewa ya rike mukamai da-dama, alhali shi kuwa Obi bai yi komai ba illa Gwamna, a cewarsa har a ilmin zamani, shi ne a kan gaba.

Jam'iyyar NNPP
Tawagar NNPP a wajen kamfe Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

“Shi Gwamna ya yi kawai, sai dai kuma ya ce shi ‘dan kasuwa ne. Ni ba haka nake ba. Ni na yi ayyuka iri-iri, kai ka sani.
Nayi aikin gwamnatin shekara 17, shi bai yi ba. Nayi mataimakin shugaban majalisa, shi bai yi ba. An zabe ni na je mun rubuta tsarin mulkin nan, shi bai yi ba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin da Ake Rigima da su a PDP Sun Hadu a Ibadan, An Samu Labarin Matsayarsu

Nayi gwamna, ya yi Gwamna. Amma ni gwamnan da na yi a Kano ne, shi kuma a Anambra ya je ya yi mulki. Ban da wannan, nayi Sanata, shi bai je Sanata ba.
Ban da wannan, na je NDDC, shi bai je NDDC ba. Ko ilminmu ka duba, za ka ga ba daya ba ne.

- Rabiu Kwankwaso

BBC ta tambayi tsohon Gwamnan ko ya yake hangen zaben 2023 musamman ganin cewa akwai yiwuwar a gagara samun wanda ya yi nasara a zagayen farko.

Rabiu Kwakwaso ya na sa ran NNPP za tayi nasara a tashin farko, ya ce idan kuwa ba haka, sauran manyan jam’iyyun da suka sha kashi za su iya taimaka masu.

Kwankwaso ya ja-kunnen Obasanjo, Clark a kan Peter Obi

Dazu ne aka ji Sanata Kwankwaso yana cewa Olusegun Obasanjo yana bata lokacinsa da ya yi wa Peter Obi mubaya'a, domin babu wanda zai saurare sa.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Babu Ruwana da Yakin Neman Zaben Bola Tinubu Inji Ministan Buhari

‘Dan takaran na NNPP mai kayan dadi ya ce duk ‘dan takaran da ya fito da fuskar ci-da-addini ko dai kabilanci, to ba zai je ko ina ba a neman shugabancin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel