Fadar Shugaban Kasa: Tsabar Takaici da Bakar Hassada Tasa Obasanjo ke Sukar Buhari

Fadar Shugaban Kasa: Tsabar Takaici da Bakar Hassada Tasa Obasanjo ke Sukar Buhari

  • Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wankin babban bargo
  • Hakan ya biyu bayan cewa da yayi shekaru 7 da rabi da suka wuce ba su yi dadi ga 'yan Najeriya ba a sakon murnar shiga sabuwar shekara da yayi wa 'yan Najeriya
  • Kakakin shugaban kasar yayin martani ga tsohon shugaban ya ce hassada ce ke dawainiya da shi duba da yadda Buhari yayi abun da ya gaza, ciki har da tazarce da ya bukaci yi

FCT, Abuja - Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, yayi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tatas bayan ya soki Buhari.

A sakonsa na murnar shiga sabuwar shekara a ranar Lahadi, Obasanjo ya soki gwamnati mai ci karkashin shugabancin Buhari, inda ya kara da cewa "shekaru bakwai da rabi da suka shude su ne shekaru marasa dadi" ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Mulkin Najeriya ba dakon siminti bane: Shettima ya yi rantsuwa, ya ce Tinubu ya fi ni koshin lafiya

Baba Buhari da Obasanjo
Fadar Shugaban Kasa: Tsabar Takaici da Bakar Hassada Tasa Obasanjo ke Sukar Buhari. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yayin martani ga sukar da yayi a wata takarda da ya fitar ranar Litinin, Shehu ya ce Obasanjo na bakin ciki saboda Buhari ya sha gaban Obasanjo a bangaren kawo cigaban kasa.

Haka zalika, Shehu ya ce Obasanjo bashi da bakin sukar mulkin Buhari, inda ya kara da cewa tsohon shugaban kasar "ya lalata asalin dimokaradiyyar" sannan "yayi amfani da mulki a inda bai dace ba" a kan wadanda yake ganin makiyansa ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Daya daga ciki shi ne, ba zai daina sukar shugaba Muhammadu Buhari ba saboda tsohon shugaban kasar ba zai daina hassada da duk wanda ya tsere masa ba a tarihin cigaban kasa,"

- Kamar yadda takardar ta bayyana.

"Shugaba Buhari ya tserewa Cif Obasanjo ta kowanne fannin cigaban kasa, kuma yin hakan kamar laifi ne ga Obasanjo wanda haukarsa ke fada masa shine shugaban da yafi kowa mulkin Najeriya yadda ya dace kuma ba za a taba yin wani wanda zai tseresa ba.

Kara karanta wannan

Yadda Kyautar Kwankwaso Ta Taimaka Mun Na Tsira Daga Harin Bam a Kaduna, Shugaba Buhari

"Yayin da ya nemi yin tazarce kuma ya gaza, karamar kwakwalwar Obasanjo dole tana fada masa shi ne ya hana shi zarcewan.
"Amma shi din ba mai hangen nesa bane kamar Buhari, a matsayinsa na shugaban kasa, Obasanjo ya rusa tushen dimokaradiyyar ta hanyar shirye sharri ga masu mulki bayan tsige gwamnonin da ba su yi amanna da mulkin kama karyarsa ba."

- Ya kara da cewa.

Kar ku bar kasar nan hannun 'yan ta'adda

A wani labari na daban, Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, ya roki jami'an tsaron Najeriya kan kada su bar kasar hannun miyagu.

Yayi kira ga jama'a da su bada gudumawa da goyon baya don ganin karshen ta'adddanci a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel